previous next

MAT 28

Tashin Yesu daga Matattu

(Mar 16.1-8; Luka 24.1-12; Yah 20.1-10)

1  t To, bayan Asabar, da asussuba a ranar farko ta mako, sai Maryamu Magadaliya da ɗaya Maryamun, suka je ganin kabarin. 2 t Sai kuwa aka yi wata babbar rawar ƙasa, domin wani mala'ikan Ubangiji ne ya sauko daga Sama, ya zo ya mirgine dutsen, ya zauna a kai. 3 t Kamanninsa suna haske kamar walƙiya, tufafinsa kuma farare fat kamar dusar ƙanƙara. 4 Saboda tsoronsa sai masu tsaro suka ɗau makyarkyata, har suka yi kamar sun mutu. 5 t Amma sai mala'ikan ya ce wa matan, “Kada ku ji tsoro, domin na sani Yesu kuke nema, wanda aka gicciye. 6 t Ai, ba ya nan. Ya tashi, yadda ya faɗa. Ku zo ku ga wurin da aka sa shi. 7 t Ku tafi maza ku gaya wa almajiransa, cewa, ya tashi daga matattu. Ga shi kuma, zai riga ku zuwa ƙasar Galili, a can ne za ku gan shi. Ga shi, na gaya muku.” 8 Sai suka tashi daga kabarin da gaggawa da tsoro, game da matuƙar farin ciki, suka ruga a guje su kai wa almajiransa labari. 9 t Sai kuwa ga Yesu ya tarye su, ya ce, “Salama alaikun!” Suka matso suka rungume ƙafafunsa, suka yi masa sujada.

10 t Sai Yesu ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ku je ku gaya wa 'yan'uwana su tafi ƙasar Galili, a can ne za su gan ni.”

Rahoton Masu Tsaron Kabarin


11  t Suna tafiya ke nan, sai waɗansu daga cikin sojan nan suka shiga birni, suka ba manyan firistoci labarin da ya auku. 12 Su kuwa da suka taru da shugabannin jama'a suka yi shawara, sai suka ba sojan kuɗi masu tsoka, 13 suka ce, “Ku faɗa wa mutane almajiransa ne suka zo da daddare suka sace shi kuna barci. 14 t In kuwa labarin nan ya kai ga kunnen mai mulki, mā rarrashe shi, mu tsare ku daga wahala.”

15 Sai suka karɓi kuɗin, suka yi yadda aka koya musu. Wannan magana kuwa, ta bazu cikin Yahudawa har ya zuwa yau.

Umarnin Yesu ga Goma Sha Ɗayan

(Mar 16.14-18; Luka 24.36-49; Yah 20.19-23)


16  t To, almajirai goma sha ɗayan nan suka tafi ƙasar Galili, suka je dutsen da Yesu ya umarce su. 17 Da suka gan shi, suka yi masa sujada, amma waɗansu suka yi shakka. 18 t Sai Yesu ya matso, ya ce musu, “An mallaka mini dukkan iko a Sama da ƙasa. 19 t Don haka sai ku je ku almajirtar da dukkan al'ummai, kuna yi musu baftisma da sunan Uba, da Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki, 20 t kuna koya musu su kiyaye duk iyakar abin da na umarce ku. Ga shi, ni kuma kullum ina tare da ku har zuwa matuƙar zamani.”

Matthew 28

1 Now late on the sabbath day, as it began to dawn toward the first day of the week, came Mary Magdalene and the other Mary to see the sepulchre.2 And behold, there was a great earthquake; for an angel of the Lord descended from heaven, and came and rolled away the stone, and sat upon it.3 His appearance was as lightning, and his raiment white as snow:4 and for fear of him the watchers did quake, and became as dead men.5 And the angel answered and said unto the women, Fear not ye; for I know that ye seek Jesus, who hath been crucified.6 He is not here; for he is risen, even as he said. Come, see the place where the Lord lay.7 And go quickly, and tell his disciples, He is risen from the dead; and lo, he goeth before you into Galilee; there shall ye see him: lo, I have told you.8 And they departed quickly from the tomb with fear and great joy, and ran to bring his disciples word.9 And behold, Jesus met them, saying, All hail. And they came and took hold of his feet, and worshipped him.10 Then saith Jesus unto them, Fear not: go tell my brethren that they depart into Galilee, and there shall they see me.

11 Now while they were going, behold, some of the guard came into the city, and told unto the chief priests all the things that were come to pass.12 And when they were assembled with the elders, and had taken counsel, they gave much money unto the soldiers,13 saying, Say ye, His disciples came by night, and stole him away while we slept.14 And if this come to the governor’s ears, we will persuade him, and rid you of care.15 So they took the money, and did as they were taught: and this saying was spread abroad among the Jews, and continueth until this day.

16 But the eleven disciples went into Galilee, unto the mountain where Jesus had appointed them.17 And when they saw him, they worshipped him; but some doubted.18 And Jesus came to them and spake unto them, saying, All authority hath been given unto me in heaven and on earth.19 Go ye therefore, and make disciples of all the nations, baptizing them into the name of the Father and of the Son and of the Holy Spirit:20 teaching them to observe all things whatsoever I commanded you: and lo, I am with you always, even unto the end of the world.