previous next

MAT 4

Shaiɗan Ya Gwada Yesu

(Mar 1.12-13; Luka 4.1-13)

1 Sa'an nan sai Ruhu ya kai Yesu cikin jeji, domin Iblis yă gwada shi. 2 t Da ya yi azumi kwana arba'in ba dare ba rana, daga baya yunwa ta kama shi. 3 t Sai Mai Gwadawar nan ya zo, ya ce masa, “In kai Ɗan Allah ne, ka umarci duwatsun nan su zama gurasa.”

4 t Amma Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake cewa,
‘Ba da gurasa kaɗai mutum zai rayu ba,
Sai dai da kowace maganar da yake fitowa daga wurin Allah.’ ”
5  t Sa'an nan Iblis ya kai shi tsattsarkan birni, ya ɗora shi can kan tsororuwar Haikali,

6 t ya ce masa, “In kai Ɗan Allah ne, to dira ƙasa. Don a rubuce yake cewa,
‘Zai yi wa mala'ikunsa umarni game da kai,’
da kuma
‘Za su tallafe ka,
Don kada ka yi tuntuɓe da dutse.’ ”
7  t Sai Yesu ya ce masa, “A rubuce yake kuma cewa, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’ ” 8 Har wa yau dai, sai Iblis ya kai shi kan wani dutse mai tsawo ƙwarai, ya nunnuna masa dukan mulkokin duniya da ɗaukakarsu. 9 Ya kuma ce masa, “Duk waɗannan zan ba ka in ka faɗi a gabana ka yi mini sujada.”

10 t Sai Yesu ya ce masa, “Tafi daga nan, kai Shaiɗan! domin a rubuce yake cewa,
‘Kă yi wa Ubangiji Allahnka sujada,
Shi kaɗai za ka bauta wa.’ ”

11  t Sa'an nan Iblis ya rabu da shi. Sai ga mala'iku sun zo suna yi masa hidima.

Yesu Ya Fara Hidima a Galili

(Mar 1.14-15; Luka 4.14-15)


12  t To, da Yesu ya ji an tsare Yahaya, sai ya tashi zuwa ƙasar Galili. 13 t Ya kuma bar Nazarat, ya koma Kafarnahum da zama, can bakin teku, a kan iyakar ƙasar Zabaluna da Naftali,

14 domin a cika faɗar Annabi Ishaya cewa,

15 “Ƙasar Zabaluna da ƙasar Naftali,
Da bakin bahar, da hayin Kogin Urdun,
Da kuma ƙasar Galili ta al'ummai,

16  t Mazaunan duhu sun ga babban haske,
Mazaunan bakin mutuwa da fargabarta,
Haske ya keto musu.”

17  t Tun daga lokacin nan, Yesu ya fara wa'azi, yana cewa, “Ku tuba domin Mulkin Sama ya kusato.”

Yesu Ya Kira Masunta Huɗu

(Mar 1.16-20; Luka 5.1-11)


18  t Yana tafiya a bakin Tekun Galili ke nan, sai ya ga waɗansu 'yan'uwa biyu, Saminu da ake kira Bitrus, da ɗan'uwansa Andarawas, suna jefa taru a teku, don su masunta ne. 19 t Sai ya ce musu, “Ku bi ni, zan mai da ku masuntan mutane.” 20 Nan da nan, sai suka watsar da tarunansu, suka bi shi. 21 t Da ya ci gaba sai ya ga waɗansu mutum biyu, su kuma 'yan'uwa ne, Yakubu ɗan Zabadi, da ɗan'uwansa Yahaya, suna cikin jirgi tare da ubansu Zabadi, suna gyaran tarunansu. Sai ya kira su.

22 Nan take suka bar jirgin duk da ubansu, suka bi shi.

Yesu Ya Hidimanta wa Mutane Masu Yawa

(Luka 6.17-19)


23  t Sai ya zazzaga duk ƙasar Galili, yana koyarwa a majami'unsu, yana shelar bisharar Mulkin Allah, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiya na mutane. 24 t Ta haka ya shahara a cikin duk ƙasar Suriya. Aka kuwa kakkawo masa dukan marasa lafiya, masu fama da cuta iri iri, da masu shan azaba, da kuma masu aljannu, da masu farraɗiya, da shanyayyu, ya kuwa warkar da su. 25 t Taro masu yawan gaske suka bi shi daga ƙasar Galili, da Dikafolis, da Urushalima, da ƙasar Yahudiya, har ma daga hayin Kogin Urdun.

Matthew 4

1 Then was Jesus led up of the Spirit into the wilderness to be tempted of the devil.2 And when he had fasted forty days and forty nights, he afterward hungered.3 And the tempter came and said unto him, If thou art the Son of God, command that these stones become bread.4 But he answered and said, It is written, Man shall not live by bread alone, but by every word that proceedeth out of the mouth of God.5 Then the devil taketh him into the holy city; and he set him on the pinnacle of the temple,6 and saith unto him, If thou art the Son of God, cast thyself down: for it is written, He shall give his angels charge concerning thee: and, On their hands they shall bear thee up, Lest haply thou dash thy foot against a stone.

7 Jesus said unto him, Again it is written, Thou shalt not make trial of the Lord thy God.8 Again, the devil taketh him unto an exceeding high mountain, and showeth him all the kingdoms of the world, and the glory of them;9 and he said unto him, All these things will I give thee, if thou wilt fall down and worship me.10 Then saith Jesus unto him, Get thee hence, Satan: for it is written, Thou shalt worship the Lord thy God, and him only shalt thou serve.11 Then the devil leaveth him; and behold, angels came and ministered unto him.

12 Now when he heard that John was delivered up, he withdrew into Galilee;13 and leaving Nazareth, he came and dwelt in Capernaum, which is by the sea, in the borders of Zebulun and Naphtali:14 that it might be fulfilled which was spoken through Isaiah the prophet, saying,

15 The land of Zebulun and the land of Naphtali, Toward the sea, beyond the Jordan, Galilee of the Gentiles,

16 The people that sat in darkness Saw a great light, And to them that sat in the region and shadow of death, To them did light spring up.

17 From that time began Jesus to preach, and to say, Repent ye; for the kingdom of heaven is at hand.

18 And walking by the sea of Galilee, he saw two brethren, Simon who is called Peter, and Andrew his brother, casting a net into the sea; for they were fishers.19 And he saith unto them, Come ye after me, and I will make you fishers of men.20 And they straightway left the nets, and followed him.21 And going on from thence he saw two other brethren, James the son of Zebedee, and John his brother, in the boat with Zebedee their father, mending their nets; and he called them.22 And they straightway left the boat and their father, and followed him.

23 And Jesus went about in all Galilee, teaching in their synagogues, and preaching the gospel of the kingdom, and healing all manner of disease and all manner of sickness among the people.24 And the report of him went forth into all Syria: and they brought unto him all that were sick, holden with divers diseases and torments, possessed with demons, and epileptic, and palsied; and he healed them.25 And there followed him great multitudes from Galilee and Decapolis and Jerusalem and Judaea and from beyond the Jordan.