MAT 5
Wa'azi a kan Dutse
(Mat 5–7)
1 Da Yesu ya ga taro masu yawa sai ya hau dutse. Da ya zauna, almajiransa kuma suka zo gunsa.
2 Sai ya buɗe baki ya koya musu.Albarku
(Luka 6.20-23)
3 t “Albarka tā tabbata ga waɗanda suka san talaucinsu na ruhu, domin Mulkin Sama nasu ne.
4 t “Albarka tā tabbata ga masu nadāma, domin za a sanyaya musu rai.
5 t “Albarka tā tabbata ga masu tawali'u, domin za su gāji duniya.
6 t “Albarka tā tabbata ga masu kwaɗaita ga adalci, domin za a biya musu muradi.
7 “Albarka tā tabbata ga majiya tausayi, domin su ma za a ji tausayinsu.
8 t “Albarka tā tabbata ga masu tsarkakakkiyar zuciya, domin za su ga Allah.
9 t “Albarka tā tabbata ga masu ƙulla zumunci, domin za a ce da su 'ya'yan Allah.
10 t “Albarka tā tabbata ga masu shan tsanani saboda aikata adalci, domin Mulkin Sama nasu ne.
11 t “Albarka tā tabbata gare ku sa'ad da mutane suka zage ku, suka tsananta muku, suka kuma ƙaga muku kowace irin mugunta, saboda ni.
12 t Ku yi murna da farin ciki matuƙa, domin sakamakonku mai yawa ne a Sama, gama haka aka tsananta wa annabawan da suka riga ku.”Gishiri da Haske
(Mar 9.50; Luka 14.34-35)
13 t “Ku ne gishirin duniya. Amma in gishiri ya sāne, da me za a daɗaɗa shi? Ba shi da sauran amfani, sai dai a zubar, mutane kuma su tattake.
14 t “Ku ne hasken duniya. Ai, birnin da aka gina bisa tudu ba shi ɓoyuwa. 15 t Ba a kunna fitila a rufe ta da masaki, sai dai a ɗora ta a kan maɗorinta, sa'an nan ta ba duk mutanen gida haske.
16 t To, haskenku yă riƙa haskakawa haka a gaban mutane, domin su ga kyawawan ayyukanku, su kuma ɗaukaka Ubanku da yake cikin Sama.”Koyarwar Yesu a kan Attaura
17 t “Kada ku yi zaton na zo ne in shafe Attaura da koyarwar annabawa. Na zo ne ba domin in shafe su ba, sai dai domin in cika su. 18 t Hakika ina gaya muku, kafin sararin sama da ƙasa su shuɗe, ko wasali ko ɗigo na Attaura ba za su shuɗe ba, sai an cika dukan kome. 19 t Don haka duk wanda ya yar da umarni ɗaya mafi ƙanƙanta daga cikin umarnan nan, har ya koya wa mutane haka, za a ce da shi mafi ƙanƙanta a Mulkin Sama. Duk wanda ya bi su kuwa, har ya koyar da su, za a ce da shi mai girma a Mulkin Sama.
20 Ina dai gaya muku, in adalcinku bai fi na malaman Attaura da Farisiyawa ba, ba za ku shiga Mulkin Sama ba faufau.”Koyarwar Yesu a kan Fushi
(Luka 12.57-59)
21 t “Kun dai ji an faɗa wa mutanen dā, ‘Kada ka yi kisankai, kowa ya yi kisa kuwa, za a hukunta shi.’ 22 t Amma ni ina gaya muku, kowa yake fushi da ɗan'uwansa ma, za a hukunta shi. Kowa ya ce da ɗan'uwansa wawa, za a kai shi gaban majalisa. Kowa kuma ya ce, ‘Kai wofi!’ hakkinsa shiga Gidan Wuta. 23 Saboda haka, in kana cikin miƙa sadakarka a kan bagadin hadaya, a nan kuma ka tuna ɗan'uwanka na da wata magana game da kai, 24 sai ka dakatar da sadakarka a gaban bagadin hadaya tukuna, ka je ku shirya da ɗan'uwanka, sa'an nan ka zo ka miƙa sadakarka. 25 Ka hanzarta shiryawa da mai ƙararka tun kuna tafiya gaban shari'a, don kada mai kararka ya bashe ka ga alƙali, alƙali kuma ya miƙa ka ga dogari, a kuma jefa ka a kurkuku.
26 Hakika ina gaya maka, ba za ka fita daga nan ba, sai ka biya duk, babu sauran ko anini.”Koyarwar Yesu a kan Zina
27 t “Kun dai ji an faɗa, ‘Kada ka yi zina.’ 28 t Amma ni ina gaya muku, kowa ya dubi mace duban sha'awa, ya riga ya yi zinar zuci ke nan da ita. 29 t In idonka na dama yana sa ka yi laifi, to, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓinka da a jefa duk jikinka ɗungum a Gidan Wuta.
30 In kuma hannunka na dama, yana sa ka yi laifi, to, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓinka da a jefa jikinka ɗungum a Gidan Wuta.”Koyarwar Yesu a kan Kisan Aure
(Mat 19.9; Mar 10.11-12; Luka 16.18)
31 t “An kuma ce, ‘Kowa ya saki matarsa, sai ya ba ta takardar saki.’
32 t Amma ni ina gaya muku, kowa ya saki matarsa, in ba a kan laifin zina ba, ya sa ta hanyar zina ke nan. Wanda kuma ya auri sakakkiya, ya yi zina.”Koyarwar Yesu a kan Rantsuwa
33 t “Har wa yau dai kun ji an faɗa wa mutanen dā, ‘Kada ka rantse a kan ƙarya, sai dai ka cika wa'adin da ka ɗaukar wa Ubangiji.’ 34 t Amma ni ina gaya muku, kada ma ku rantse sam, ko da sama, domin ita ce kursiyin Allah, 35 t ko da ƙasa, domin ita ce matashin ƙafarsa, ko kuma da Urushalima, domin ita ce birnin Babban Sarki. 36 Kada kuwa ka rantse da kanka, don ba za ka iya mai da ko gashi ɗaya fari ko baƙi ba.
37 t Abin da duk za ku faɗa ya tsaya a kan ‘I’ ko ‘A'a’ kawai. In dai ya zarce haka, to, daga Mugun ya fito.”Koyarwar Yesu a kan Ramawa
(Luka 6.29-30)
38 t “Kun dai ji an faɗa, ‘Sakayyar ido, ido ne, sakayyar haƙori kuma haƙori ne.’ 39 t Amma ni ina gaya muku, kada ku ƙi a cuce ku. Amma ko wani ya mare ka a kuncin dama, to, juya masa ɗayan kuma. 40 In kuwa wani ya yi ƙararka da niyyar karɓe taguwarka, to, ka bar masa mayafinka ma. 41 In kuma wani ya tilasta maka ku yi tafiyar mil guda tare, to, ku yi tafiyar mil biyu ma.
42 t Kowa ya roƙe ka, ka ba shi, mai neman rance a wurinka kuwa, kada ka hana shi.”Ƙaunar Magabta
(Luka 6.27-28, 32-36)
43 t “Kun dai ji an faɗa, ‘Ka so ɗan'uwanka, ka ƙi magabcinka.’ 44 t Amma ni ina gaya muku, ku ƙaunaci magabtanku, ku yi wa masu tsananta muku addu'a, 45 t domin ku zama 'ya'yan Ubanku wanda yake cikin Sama. Domin yakan sa rana tasa ta fito kan mugaye da kuma nagargaru, ya kuma sako ruwan sama ga masu adalci da marasa adalci. 46 t In masoyanku kawai kuke ƙauna, wane lada ne da ku? Ashe, ko masu karɓar haraji ma ba haka suke yi ba? 47 In kuwa 'yan'uwanku kaɗai kuke gayarwa, me kuka yi fiye da waɗansu? Ashe, ko al'ummai ma ba haka suke yi ba? 48 t Saboda haka sai ku zama cikakku, kamar yadda Ubanku na Sama take cikakke.”
Matthew 5
1 And seeing the multitudes, he went up into the mountain: and when he had sat down, his disciples came unto him:2 and he opened his mouth and taught them, saying,
3 Blessed are the poor in spirit: for theirs is the kingdom of heaven.
4 Blessed are they that mourn: for they shall be comforted.
5 Blessed are the meek: for they shall inherit the earth.
6 Blessed are they that hunger and thirst after righteousness: for they shall be filled.
7 Blessed are the merciful: for they shall obtain mercy.
8 Blessed are the pure in heart: for they shall see God.
9 Blessed are the peacemakers: for they shall be called sons of God.
10 Blessed are they that have been persecuted for righteousness’ sake: for theirs is the kingdom of heaven.11 Blessed are ye when men shall reproach you, and persecute you, and say all manner of evil against you falsely, for my sake.12 Rejoice, and be exceeding glad: for great is your reward in heaven: for so persecuted they the prophets that were before you.
13 Ye are the salt of the earth: but if the salt have lost its savor, wherewith shall it be salted? it is thenceforth good for nothing, but to be cast out and trodden under foot of men.14 Ye are the light of the world. A city set on a hill cannot be hid.15 Neither do men light a lamp, and put it under the bushel, but on the stand; and it shineth unto all that are in the house.16 Even so let your light shine before men; that they may see your good works, and glorify your Father who is in heaven.
17 Think not that I came to destroy the law or the prophets: I came not to destroy, but to fulfil.18 For verily I say unto you, Till heaven and earth pass away, one jot or one tittle shall in no wise pass away from the law, till all things be accomplished.19 Whosoever therefore shall break one of these least commandments, and shall teach men so, shall be called least in the kingdom of heaven: but whosoever shall do and teach them, he shall be called great in the kingdom of heaven.20 For I say unto you, that except your righteousness shall exceed the righteousness of the scribes and Pharisees, ye shall in no wise enter into the kingdom of heaven.
21 Ye have heard that it was said to them of old time, Thou shalt not kill; and whosoever shall kill shall be in danger of the judgment:22 but I say unto you, that every one who is angry with his brother shall be in danger of the judgment; and whosoever shall say to his brother, Raca, shall be in danger of the council; and whosoever shall say, Thou fool, shall be in danger of the hell of fire.23 If therefore thou art offering thy gift at the altar, and there rememberest that thy brother hath aught against thee,24 leave there thy gift before the altar, and go thy way, first be reconciled to thy brother, and then come and offer thy gift.25 Agree with thine adversary quickly, while thou art with him in the way; lest haply the adversary deliver thee to the judge, and the judge deliver thee to the officer, and thou be cast into prison.26 Verily I say unto thee, thou shalt by no means come out thence, till thou have paid the last farthing.
27 Ye have heard that it was said, Thou shalt not commit adultery:28 but I say unto you, that every one that looketh on a woman to lust after her hath committed adultery with her already in his heart.29 And if thy right eye causeth thee to stumble, pluck it out, and cast it from thee: for it is profitable for thee that one of thy members should perish, and not thy whole body be cast into hell.30 And if thy right hand causeth thee to stumble, cut it off, and cast it from thee: for it is profitable for thee that one of thy members should perish, and not thy whole body go into hell.31 It was said also, Whosoever shall put away his wife, let him give her a writing of divorcement:32 but I say unto you, that every one that putteth away his wife, saving for the cause of fornication, maketh her an adulteress: and whosoever shall marry her when she is put away committeth adultery.
33 Again, ye have heard that it was said to them of old time, Thou shalt not forswear thyself, but shalt perform unto the Lord thine oaths:34 but I say unto you, swear not at all; neither by the heaven, for it is the throne of God;35 nor by the earth, for it is the footstool of his feet; nor by Jerusalem, for it is the city of the great King.36 Neither shalt thou swear by thy head, for thou canst not make one hair white or black.37 But let your speech be, Yea, yea; Nay, nay: and whatsoever is more than these is of the evil one.
38 Ye have heard that it was said, An eye for an eye, and a tooth for a tooth:39 but I say unto you, resist not him that is evil: but whosoever smiteth thee on thy right cheek, turn to him the other also.40 And if any man would go to law with thee, and take away thy coat, let him have thy cloak also.41 And whosoever shall compel thee to go one mile, go with him two.42 Give to him that asketh thee, and from him that would borrow of thee turn not thou away.
43 Ye have heard that it was said, Thou shalt love thy neighbor, and hate thine enemy:44 but I say unto you, love your enemies, and pray for them that persecute you;45 that ye may be sons of your Father who is in heaven: for he maketh his sun to rise on the evil and the good, and sendeth rain on the just and the unjust.46 For if ye love them that love you, what reward have ye? do not even the publicans the same?47 And if ye salute your brethren only, what do ye more than others? do not even the Gentiles the same?48 Ye therefore shall be perfect, as your heavenly Father is perfect.