previous next

MAT 6

Koyarwar Yesu a kan Ba Da Sadaka

1  t “Ku yi hankali kada ibadarku ta zama ta ganin ido. Domin in kun yi haka, ba za ku sami sakamako wurin Ubanku da yake a Sama ba.
2 “Wato, in za ka yi sadaka, kada ka yi kwakwazo yadda munafukai suke yi a majami'u da kuma kan hanya don dai mutane su yabe su. Gaskiya nake faɗa muku, sun sami iyakar ladarsu ke nan. 3 Amma in kana yin sadaka, kada hannunka na hagu ya san abin da hannunka na dama yake yi,

4 t domin sadakarka tă zama a asirce, Ubanku kuwa da yake ganin abin da ake yi a asirce, zai sāka maka.”

Koyarwar Yesu a kan Addu'a

(Luka 11.2-4)


5  t “In za ku yi addu'a, kada ku zama kamar munafukai, don sun cika son yin addu'a a tsaye a majami'u da kan hanya, wai mutane su gan su. Gaskiya nake gaya muku, sun sami iyakar ladansu.

6 t Amma in za ka yi addu'a, sai ka shiga lollokinka, ka rufe ƙofa, ka yi addu'a ga Ubanku wanda yake ɓoye, Ubanku kuwa da yake ganin abin da ake yi a asirce, zai sāka maka.
7  t “In kuwa kuna addu'a, kada ku yi ta maimaitawar banza, kamar yadda al'ummai suke yi, a zatonsu za a saurare su saboda yawan maganarsu. 8 t Kada ku zama kamarsu, domin Ubanku ya san bukatarku tun kafin ku roƙe shi.

9 Saboda haka sai ku yi addu'a kamar haka,
‘Ya Ubanmu, wanda yake cikin Sama,
A kiyaye sunanka da tsarki.

10  t Mulkinka yă zo,
A aikata nufinka a duniya kamar yadda ake yi a Sama.

11  t Ka ba mu abincinmu na yau.

12  t Ka gafarta mana laifofinmu,
Kamar yadda mu ma muke gafarta wa waɗanda suke yi mana laifi.

13  t Kada ka kai mu wurin jaraba,
Amma ka cece mu daga Mugun.’
14  t Domin in kun yafe wa mutane laifofinsu, Ubanku na Sama zai yafe muku.

15 t In kuwa ba ku yafe wa mutane laifofinsu ba, Ubanku ma ba zai yafe muku naku ba.”

Koyarwar Yesu a kan Azumi


16  t “In kuma kuna yin azumi, kada ku turɓune fuska kamar munafukai, don sukan yanƙwane fuska, wai don mutane su ga suna azumi ne. Hakika, ina gaya muku, sun sami iyakar ladansu ke nan. 17 Amma in kana azumi, ka shafa mai a ka, ka kuma wanke fuska,

18 t don kada mutane su ga alama kana azumi, sai dai Ubanku da yake ɓoye ya gani. Ubanku kuma da yake ganin abin da ake yi a asirce, zai sāka maka.”

Tara Dukiya a Sama

(Luka 12.33-34)


19  t “Kada ku tara wa kanku dukiya a duniya, inda asu da tsatsa suke ɓatawa, inda ɓarayi kuma suke karyawa su yi sata. 20 t Sai dai ku tara wa kanku dukiya a Sama, inda ba asu da tsatsa da za su ɓata, inda kuma ba ɓarayin da za su karya su yi sata.

21 t Domin kuwa inda dukiyarka take, a nan zuciyarka ma take.”

Fitilar Jiki

(Luka 11.34-36)


22 “Ido shi ne fitilar jiki. In idonka lafiyayye ne, duk jikinka ma sai ya cika da haske.

23 In kuwa idonka da lahani, duk jikinka sai ya cika da duhu. To, in hasken da yake gare ka duhu ne, ina misalin yawan duhun!”

Bauta wa Allah ko Dukiya

(Luka 16.13)


24  t “Ba mai iya bauta wa iyayengiji biyu; ko dai ya ƙi ɗaya, ya so ɗaya, ko kuwa ya amince wa ɗayan, ya raina ɗayan. Ba dama ku bauta wa Allah da dukiya gaba ɗaya.”

Damuwa da Alhini

(Luka 12.22-31)


25  t “Saboda haka ina gaya muku, kada ku damu a kan rayuwarku game da abin da za ku ci, da abin da za ku sha, ko kuwa jikinku, abin da za ku yi sutura. Ashe, rai bai fi abinci ba? Jiki kuma bai fi tufafi ba? 26 t Ku dubi dai tsuntsaye. Ai, ba sa shuka, ba sa girbi, ba sa kuma tarawa a rumbuna, amma kuwa Ubanku na Sama na ci da su. Ashe, ko ba ku fi martaba nesa ba? 27 t Wane ne a cikinku, don damuwarsa, zai iya ƙara ko da taƙi ga tsawon rayuwarsa? 28 To, don me kuke damuwa a kan tufafi? Ku dubi dai furannin jeji, yadda suke girma, ba sa aikin fari, ba sa na baƙi, 29 t duk da haka ina gaya muku, ko Sulemanu ma, shi da adonsa duk, bai taɓa yin adon da ya fi na ɗayansu ba. 30 t To, ga shi, Allah yana ƙawata tsire-tsiren jeji ma haka, waɗanda yau suke raye, gobe kuwa a jefa su a murhu, balle ku? Ya ku masu ƙarancin bangaskiya! 31 Don haka kada ku damu, kuna cewa, ‘Me za mu ci?’ ko, ‘Me za mu sha?’ ko kuwa, ‘Me za mu sa?’ 32 t Ai, al'ummai ma suna ta neman duk irin waɗannan abubuwa, Ubanku na Sama kuwa ya san kuna bukatarsu duka.

33 t Muhimmin abu na farko, sai ku ƙwallafa rai ga al'amuran Mulkin Allah, da kuma adalcinsa, har ma za a ƙara muku dukan waɗannan abubuwa.
34 “Saboda haka kada ku damu don gobe, ai, gobe ta Allah ce. Wahalce-wahalcen yau ma sun isa wahala.”

Matthew 6

1 Take heed that ye do not your righteousness before men, to be seen of them: else ye have no reward with your Father who is in heaven.2 When therefore thou doest alms, sound not a trumpet before thee, as the hypocrites do in the synagogues and in the streets, that they may have glory of men. Verily I say unto you, They have received their reward.3 But when thou doest alms, let not thy left hand know what thy right hand doeth:4 that thine alms may be in secret: and thy Father who seeth in secret shall recompense thee.

5 And when ye pray, ye shall not be as the hypocrites: for they love to stand and pray in the synagogues and in the corners of the streets, that they may be seen of men. Verily I say unto you, They have received their reward.6 But thou, when thou prayest, enter into thine inner chamber, and having shut thy door, pray to thy Father who is in secret, and thy Father who seeth in secret shall recompense thee.7 And in praying use not vain repetitions, as the Gentiles do: for they think that they shall be heard for their much speaking.8 Be not therefore like unto them: for your Father knoweth what things ye have need of, before ye ask him.9 After this manner therefore pray ye. Our Father who art in heaven, Hallowed be thy name.10 Thy kingdom come. Thy will be done, as in heaven, so on earth.11 Give us this day our daily bread.12 And forgive us our debts, as we also have forgiven our debtors.13 And bring us not into temptation, but deliver us from the evil one.14 For if ye forgive men their trespasses, your heavenly Father will also forgive you.15 But if ye forgive not men their trespasses, neither will your Father forgive your trespasses.

16 Moreover when ye fast, be not, as the hypocrites, of a sad countenance: for they disfigure their faces, that they may be seen of men to fast. Verily I say unto you, They have received their reward.17 But thou, when thou fastest, anoint thy head, and wash thy face;18 that thou be not seen of men to fast, but of thy Father who is in secret: and thy Father, who seeth in secret, shall recompense thee.

19 Lay not up for yourselves treasures upon the earth, where moth and rust consume, and where thieves break through and steal:20 but lay up for yourselves treasures in heaven, where neither moth nor rust doth consume, and where thieves do not break through nor steal:21 for where thy treasure is, there will thy heart be also.22 The lamp of the body is the eye: if therefore thine eye be single, thy whole body shall be full of light.23 But if thine eye be evil, thy whole body shall be full of darkness. If therefore the light that is in thee be darkness, how great is the darkness!24 No man can serve two masters; for either he will hate the one, and love the other; or else he will hold to one, and despise the other. Ye cannot serve God and mammon.25 Therefore I say unto you, be not anxious for your life, what ye shall eat, or what ye shall drink; nor yet for your body, what ye shall put on. Is not the life more than the food, and the body than the raiment?26 Behold the birds of the heaven, that they sow not, neither do they reap, nor gather into barns; and your heavenly Father feedeth them. Are not ye of much more value then they?27 And which of you by being anxious can add one cubit unto the measure of his life?28 And why are ye anxious concerning raiment? Consider the lilies of the field, how they grow; they toil not, neither do they spin:29 yet I say unto you, that even Solomon in all his glory was not arrayed like one of these.30 But if God doth so clothe the grass of the field, which to-day is, and to-morrow is cast into the oven, shall he not much more clothe you, O ye of little faith?31 Be not therefore anxious, saying, What shall we eat? or, What shall we drink? or, Wherewithal shall we be clothed?32 For after all these things do the Gentiles seek; for your heavenly Father knoweth that ye have need of all these things.33 But seek ye first his kingdom, and his righteousness; and all these things shall be added unto you.34 Be not therefore anxious for the morrow: for the morrow will be anxious for itself. Sufficient unto the day is the evil thereof.