MAT 7
Kada Ku Ɗora wa Kowa Laifi
(Luka 6.37-38, 41-42)
1 t “Kada ku ɗora wa kowa laifi, don kada a ɗora muku. 2 t Don da irin hukuncin da kuka zartar, da shi za a zartar muku. Mudun da kuka auna, da shi za a auna muku. 3 Don me kake duban ɗan hakin da yake idon ɗan'uwanka, amma gungumen da yake a naka ido ba ka kula ba? 4 Ko kuwa yaya za ka iya ce wa ɗan'wanka, ‘Bari in cire maka ɗan hakin daga idonka,’ alhali kuwa da gungume a naka ido?
5 Kai munafuki! Sai ka fara cire gungumen da yake idonka tukuna, sa'an nan ka gani sosai yadda za ka cire ɗan hakin daga idon ɗan'uwanka.
6 “Kada ku ba karnuka abin da yake tsattsarka. Kada kuma ku jefa wa alhanzir lu'ulu'unku, don kada su tattake su, su juyo su kyakketa ku.”Ku Roƙa, Ku Nema, Ku Ƙwanƙwasa
(Luka 11.9-13)
7 t “Ku yi ta roƙo, za a ba ku. Ku yi ta nema, za ku samu. Ku yi ta ƙwanƙwasawa, za a kuwa buɗe muku. 8 t Duk wanda ya roƙa, akan ba shi, mai nema yana tare da samu. Wanda ya ƙwanƙwasa kuma za a buɗe masa. 9 To, wane ne a cikinku, ɗansa zai roƙe shi gurasa, ya ba shi dutse? 10 Ko kuwa ya roƙe shi kifi, ya ba shi maciji? 11 To, ku da kuke mugaye ma, kuka san yadda za ku ba 'ya'yanku kyautar kyawawan abubuwa, balle Ubanku na Sama da zai ba da abubuwan alheri ga masu roƙonsa?
12 t Saboda haka duk abin da kuke so mutane su yi muku, ku ma sai ku yi musu, domin wannan shi ne Attaura da koyarwar annabawa.”Ƙunƙuntar Ƙofa
(Luka 13.24)
13 t “Ku shiga ta ƙunƙuntar ƙofa, gama ƙofa zuwa hallaka faffaɗa ce, hanyarta mai sauƙin bi ce, masu shiga ta cikinta suna da yawa.
14 Domin kuwa ƙofar zuwa rai ƙunƙunta ce, hanyarta mai wuyar bi ce, masu samunta kuwa kaɗan ne.”Akan Gane Itace ta 'Ya'yansa
(Luka 6.43-44)
15 t “Ku kula da annabawan ƙarya, waɗanda sukan zo muku da siffar tumaki, amma a zuci kyarketai ne masu ƙāwa. 16 t Za ku gane su ta irin aikinsu. A iya ciran inabi a jikin ƙaya, ko kuwa ɓaure a jikin sarƙaƙƙiya? 17 Haka kowane itacen kirki yakan haifi kyawawan 'ya'ya. Mummunan itace kuwa yakan haifi munanan 'ya'ya. 18 Kyakkyawan itace ba dama ya haifi munanan 'ya'ya. Haka kuma mummunan itace ba dama ya haifi kyawawan 'ya'ya. 19 t Duk itacen da ba ya 'ya'ya masu kyau, sai a sare shi a jefa a wuta.
20 Don haka, da irin aikinsu za a gane su.”Ban Taɓa Saninku ba
(Luka 13.25-27)
21 t “Ba duk mai ce mini, ‘Ya Ubangiji, ya Ubangiji,’ ne zai shiga Mulkin Sama ba, sai dai wanda ya yi abin da Ubana da yake cikin Sama yake so. 22 t A ranar nan da yawa za su ce mini, ‘Ya Ubangiji, ya Ubangiji, ashe, ba mu yi annabci da sunanka ba? Ba mu fitar da aljannu da sunanka ba? Ba mu kuma yi ayyukan al'ajabi masu yawa da sunanka ba?’
23 t Sa'an nan zan ce musu, ‘Ni ban taɓa saninku ba. Ku rabu da ni, ku masu yin mugun aiki.’ ”Kafa Harsashin Gini Iri Biyu
(Luka 6.47-49)
24 t “Saboda haka, kowa da yake jin maganar nan tawa, yake kuma aikata ta, za a kwatanta shi da mutum mai hikima, wanda ya gina gidansa a kan fā. 25 Da ruwa ya sauko, koguna suka yi cikowa, iska ta taso ta bugi gidan, amma bai faɗi ba, domin an gina shi a kan fā ne. 26 Kowa ya ji maganar nan tawa, bai aikata ta kuma ba, za a misalta shi da wawan mutum, wanda ya gina gidansa a kan rairayi.
27 Da ruwa ya sauko, koguna suka yi cikowa, sai iska ta taso ta bugi gidan har ya rushe, mummunar ragargajewa kuwa!”Hakikancewar Yesu
(Mar 1.22)
28 t Da Yesu ya gama duk wannan magana, sai taro suka yi mamakin koyarwarsa, 29 domin yana koya musu da hakikancewa, ba kamar malamansu na Attaura ba.
Matthew 7
1 Judge not, that ye be not judged.2 For with what judgment ye judge, ye shall be judged: and with what measure ye mete, it shall be measured unto you.3 And why beholdest thou the mote that is in thy brother’s eye, but considerest not the beam that is in thine own eye?4 Or how wilt thou say to thy brother, Let me cast out the mote out of thine eye; and lo, the beam is in thine own eye?5 Thou hypocrite, cast out first the beam out of thine own eye; and then shalt thou see clearly to cast out the mote out of thy brother’s eye.
6 Give not that which is holy unto the dogs, neither cast your pearls before the swine, lest haply they trample them under their feet, and turn and rend you.
7 Ask, and it shall be given you; seek, and ye shall find; knock, and it shall be opened unto you:8 for every one that asketh receiveth; and he that seeketh findeth; and to him that knocketh it shall be opened.9 Or what man is there of you, who, if his son shall ask him for a loaf, will give him a stone;10 or if he shall ask for a fish, will give him a serpent?11 If ye then, being evil, know how to give good gifts unto your children, how much more shall your Father who is in heaven give good things to them that ask him?12 All things therefore whatsoever ye would that men should do unto you, even so do ye also unto them: for this is the law and the prophets.
13 Enter ye in by the narrow gate: for wide is the gate, and broad is the way, that leadeth to destruction, and many are they that enter in thereby.14 For narrow is the gate, and straitened the way, that leadeth unto life, and few are they that find it.
15 Beware of false prophets, who come to you in sheep’s clothing, but inwardly are ravening wolves.16 By their fruits ye shall know them. Do men gather grapes of thorns, or figs of thistles?17 Even so every good tree bringeth forth good fruit; but the corrupt tree bringeth forth evil fruit.18 A good tree cannot bring forth evil fruit, neither can a corrupt tree bring forth good fruit.19 Every tree that bringeth not forth good fruit is hewn down, and cast into the fire.20 Therefore by their fruits ye shall know them.21 Not every one that saith unto me, Lord, Lord, shall enter into the kingdom of heaven; but he that doeth the will of my Father who is in heaven.22 Many will say to me in that day, Lord, Lord, did we not prophesy by thy name, and by thy name cast out demons, and by thy name do many mighty works?23 And then will I profess unto them, I never knew you: depart from me, ye that work iniquity.
24 Every one therefore that heareth these words of mine, and doeth them, shall be likened unto a wise man, who built his house upon the rock:25 and the rain descended, and the floods came, and the winds blew, and beat upon that house; and if fell not: for it was founded upon the rock.26 And every one that heareth these words of mine, and doeth them not, shall be likened unto a foolish man, who built his house upon the sand:27 and the rain descended, and the floods came, and the winds blew, and smote upon that house; and it fell: and great was the fall thereof.
28 And it came to pass, when Jesus had finished these words, the multitudes were astonished at his teaching:29 for he taught them as one having authority, and not as their scribes.