previous next

FILIB 1

Gaisuwa

1  t Daga Bulus da Timoti, bayin Almasihu Yesu, zuwa ga dukan tsarkaka a cikin Almasihu Yesu waɗanda suke a Filibi, tare da masu kula da ikkilisiya da kuma masu hidimarta.

2  t Alheri da salama na Allah ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu, su tabbata a gare ku.

Addu'ar Bulus domin Filibiyawa Masu Bin Almasihu


3  t Ina gode Allahna duk sa'ad da nake tunawa da ku, 4 t a kullum kuwa a kowace addu'a da nake muku duka, da farin ciki nake yi. 5 t Ina godiya saboda tarayyarku da ni wajen yaɗa bishara, tun daga ranar farko har ya zuwa yanzu. 6 t Na tabbata shi wanda ya fara kyakkyawan aiki a gare ku, zai ƙarasa shi, har ya zuwa ranar Yesu Almasihu. 7 t Daidai ne kuwa a gare ni in riƙa tunaninku haka, ku duka, domin kuna a cikin zuciyata, domin dukanku abokan tarayya ne da ni da alherin Allah, ta wajen ɗaure ni da aka yi, da kuma ta yin kāriyar bishara da tabbatar da ita. 8 t Domin Allah shi ne mashaidina a kan yadda nake begenku duka, da irin ƙaunar da Almasihu Yesu yake yi. 9 t Addu'ata ita ce, ƙaunarku ta riƙa haɓaka da sani da matuƙar ganewa, 10 t domin ku zaɓi abubuwa mafifita, ku zama sahihai, marasa abin zargi, har ya zuwa ranar Almasihu,

11 t kuna da cikakken sakamakon aikin adalci da yake samuwa ta wurin Yesu Almasihu, wannan kuwa duk domin ɗaukakar Allah ne, da yabonsa.

Manufar Rayuwata, Almasihu Ne


12 'Yan'uwa, ina so ku sani, al'amuran nan da suka auku a gare ni, har ma sun yi amfani wajen yaɗa bishara, 13 t har dai ya zama sananne ga dukan sojan fāda da sauran jama'a, cewa ɗaurina saboda Almasihu ne.

14 t Har ma galibin 'yan'uwa cikin Ubangiji suka ƙarfafa saboda ɗaurina, sun kuma ƙara fitowa gabagaɗi, su faɗi Maganar Allah ba tare da tsoro ba.
15 Lalle waɗansu suna wa'azin Almasihu saboda hassada da husuma, amma waɗansu kam, saboda kyakkyawar niyya ne. 16 t Waɗannan suna yi ne a kan ƙauna, sun sani, an sa ni nan ne domin kāriyar bishara.

17 t Waɗancan kuwa suna shelar Almasihu saboda sonkai ne, ba da zuciya ɗaya ba, a sonsu, su wahalar da ni a cikin ɗaurina.
18 Me kuma? Ta ko yaya dai, ko da gangan, ko da gaske, ana shelar Almasihu, na kuma yi farin ciki da haka. I, zan yi farin ciki kuwa. 19 t Domin na san duk wannan zai zama sanadin lafiyata, ta wurin addu'arku da taimakon Ruhun Yesu Almasihu. 20 t Don kuwa ina ɗoki, ina kuma sa zuciya, ko kaɗan ba zan kunyata ba, sai dai zan yi ƙarfin hali matuƙa a yanzu kamar koyaushe, a girmama Almasihu a jikina, ko ta wurin rayuwata, ko ta wurin mutuwata. 21 t Domin ni, a gare ni, rai Almasihu ne, mutuwa kuwa riba ce. 22 In ya zamanto rayuwa zan yi a cikin jiki, to, zan yi aiki mai amfani ke nan. Amma na rasa abin da zan zaɓa. 23 t Duka biyu suna jan hankalina ƙwarai. Burina in ƙaura in zauna tare da Almasihu, domin wannan shi ne ya fi kyau nesa. 24 Amma in wanzu a cikin jiki, shi ya fi wajabta saboda ku. 25 Na tabbata haka ne, na kuwa sani zan wanzu in zauna tare da ku duka, domin ku ci gaba, bangaskiyarku tana sa ku yin farin ciki,

26 ku kuma sami ƙwaƙƙwaran dalilin yin taƙama da Almasihu ta wurina, saboda sāke komowata gare ku.
27  t Sai dai ku yi zaman da ya cancanci bisharar Almasihu, domin ko na zo na gan ku, ko kuwa ba na nan, in ji labarinku, cewa kun dage, nufinku ɗaya, ra'ayinku ɗaya, kuna fama tare saboda bangaskiyar da bishara take sawa, 28 ba kwa kuwa jin tsoron magabtanku sam. Wannan kuwa ishara ce a gare su ta hallakarsu, ku kuwa ta cetonku, isharar kuwa daga Allah take. 29 t Gama an yi muku alheri, cewa ba gaskatawa da Almasihu kawai za ku yi ba, har ma za ku sha wuya dominsa, 30 t kuna shan fama irin nawa wanda kuka gani, wanda kuke ji nake sha har yanzu.

Philippians 1

1 Paul and Timothy, servants of Christ Jesus, to all the saints in Christ Jesus that are at Philippi, with the bishops and deacons:2 Grace to you and peace from God our Father and the Lord Jesus Christ.3 I thank my God upon all my remembrance of you,4 always in every supplication of mine on behalf of you all making my supplication with joy,5 for your fellowship in furtherance of the gospel from the first day until now;6 being confident of this very thing, that he who began a good work in you will perfect it until the day of Jesus Christ:7 even as it is right for me to be thus minded on behalf of you all, because I have you in my heart, inasmuch as, both in my bonds and in the defence and confirmation of the gospel, ye all are partakers with me of grace.8 For God is my witness, how I long after you all in the tender mercies of Christ Jesus.9 And this I pray, that your love may abound yet more and more in knowledge and all discernment;10 so that ye may approve the things that are excellent; that ye may be sincere and void of offence unto the day of Christ;11 being filled with the fruits of righteousness, which are through Jesus Christ, unto the glory and praise of God.12 Now I would have you know, brethren, that the things which happened unto me have fallen out rather unto the progress of the gospel;13 so that my bonds became manifest in Christ throughout the whole praetorian guard, and to all the rest;14 and that most of the brethren in the Lord, being confident through my bonds, are more abundantly bold to speak the word of God without fear.15 Some indeed preach Christ even of envy and strife; and some also of good will:16 the one do it of love, knowing that I am set for the defence of the gospel;17 but the other proclaim Christ of faction, not sincerely, thinking to raise up affliction for me in my bonds.18 What then? only that in every way, whether in pretence or in truth, Christ is proclaimed; and therein I rejoice, yea, and will rejoice.19 For I know that this shall turn out to my salvation, through your supplication and the supply of the Spirit of Jesus Christ,20 according to my earnest expectation and hope, that in nothing shall I be put to shame, but that with all boldness, as always, so now also Christ shall be magnified in my body, whether by life, or by death.21 For to me to live is Christ, and to die is gain.22 But if to live in the flesh, --if this shall bring fruit from my work, then what I shall choose I know not.23 But I am in a strait betwixt the two, having the desire to depart and be with Christ; for it is very far better:24 yet to abide in the flesh is more needful for your sake.25 And having this confidence, I know that I shall abide, yea, and abide with you all, for your progress and joy in the faith;26 that your glorying may abound in Christ Jesus in me through my presence with you again.27 Only let your manner of life be worthy of the gospel of Christ: that, whether I come and see you and be absent, I may hear of your state, that ye stand fast in one spirit, with one soul striving for the faith of the gospel;28 and in nothing affrighted by the adversaries: which is for them an evident token of perdition, but of your salvation, and that from God;29 because to you it hath been granted in the behalf of Christ, not only to believe on him, but also to suffer in his behalf:30 having the same conflict which ye saw in me, and now hear to be in me.