FILIB 2
Ƙasƙantar Almasihu da kuma Ɗaukakarsa
1 t In akwai ƙarfafawa a cikin Almasihu, in dai da ƙarfin rinjaye na ƙauna, in har da tarayyarku ga Ruhu, da soyayyarku da kuma tausayinku, 2 t to, albarkacinsu ku cikasa farin cikina da zamanku lafiya da juna, kuna ƙaunar juna, nufinku ɗaya, ra'ayinku ɗaya. 3 t Kada ku yi kome da sonkai ko girmankai, sai dai da tawali'u, kowa yana mai da ɗan'uwansa ya fi shi.
4 Kowannenku kada ya kula da harkar kansa kawai, sai dai ya kula har da ta ɗan'uwansa ma.
5 t Ku ɗauki halin Almasihu Yesu, 6 t wanda, ko da yake a cikin surar Allah yake, bai mai da daidaitakar nan tasa da Allah abar da zai riƙe kankan ce ba, 7 t sai ma ya mai da kansa baya matuƙa ta ɗaukar surar bawa, da kuma kasancewa da kamannin ɗan adam. 8 t Da ya bayyana da siffar mutum, sai ya ƙasƙantar da kansa ta wurin yin biyayya, har wadda ta kai shi ga mutuwa, mutuwar ma ta gicciye. 9 t Saboda haka ne kuma Allah ya ɗaukaka shi mafificiyar ɗaukaka, ya kuma yi masa baiwa da sunan nan da yake birbishin kowane suna, 10 t domin dai kowace gwiwa sai ta rusuna wa sunan nan na Yesu, a Sama da ƙasa, da kuma can ƙarƙashin ƙasa,
11 t kowane harshe kuma yă shaida Yesu Almasihu Ubangiji ne, domin ɗaukaka Allah Uba.Haskakawa Kamar Fitilu a Duniya
12 t Saboda haka, ya ƙaunatattuna, kamar yadda a kullum kuke biyayya, haka kuma yanzu, ku yi ta yin aikin ceton nan naku da halin bangirma tare da matsananciyar kula, ba ma sai ina nan kawai ba, har ma fiye da haka in ba na nan.
13 t Domin Allah shi ne mai aiki a zukatanku, ku nufi abin da yake kyakkyawan nufinsa, ku kuma aikata shi.
14 t Kome za ku yi, kada ku yi da gunaguni, ko gardama, 15 t don ku zama marasa abin zargi, sahihai, 'ya'yan Allah marasa aibu, a zamanin mutane karkatattu, kangararru, waɗanda kuke haskakawa a cikinsu kamar fitilu a duniya, 16 t kuna riƙe da maganar rai kankan, har a ranar bayyanar Almasihu in yi taƙama, cewa himmata da famana ba a banza suke ba. 17 t Ko da za a tsiyaye jinina a kan hadaya da hidima na bangaskiyarku, sai in yi farin ciki, in kuma taya ku farin ciki, ku duka.
18 Haka ku ma, ya kamata ku yi farin ciki, ku kuma taya ni farin ciki.Timoti da Abafaroditas
19 t Ina sa zuciya ga Ubangiji Yesu in aika muku da Timoti da wuri, don ni ma in ƙarfafa da samun labarinku. 20 t Ba ni da wani kamarsa, wanda da sahihanci zai tsananta kula da zamanku lafiya. 21 t Dukansu sha'anin gabansu kawai suke yi, ba na Yesu Almasihu ba. 22 t Amma, ai, kun san darajar Timoti yadda muka yi bautar bishara tare, kamar ɗa da mahaifinsa. 23 t Shi ne nake fata in aiko, da zarar na ga yadda al'amarina yake gudana.
24 t Na kuma amince har ga Ubangiji, ni ma da kaina ina zuwa ba da daɗewa ba.
25 t Amma na ga lalle ne in aiko muku da Abafaroditas ɗan'uwana, abokin aikina, abokin famana kuma, wanda kuka aiko ya yi mini ɗawainiya. 26 t Yana begenku ku duka, har ma ya damu ƙwarai don kun ji ba shi da lafiya. 27 Lalle ya yi rashin lafiya, har ya yi kusan mutuwa. Amma Allah ya ji tausayinsa, ba kuwa shi kaɗai ba, har ni ma, don kada in yi baƙin ciki a kan baƙin ciki. 28 Saboda haka na ɗokanta ƙwarai in turo shi domin ku yi farin cikin sāke ganinsa, ni kuma in rage baƙin cikina. 29 t Don haka sai ku karɓe shi da matuƙar farin ciki saboda Ubangiji, ku kuma girmama irin waɗannan mutane, 30 t domin ya kusa ya mutu saboda aikin Almasihu, yana sai da ransa domin ya cikasa ɗawainiyarku gare ni.
Philippians 2
1 If there is therefore any exhortation in Christ, if any consolation of love, if any fellowship of the Spirit, if any tender mercies and compassions,2 make full my joy, that ye be of the same mind, having the same love, being of one accord, of one mind;3 doing nothing through faction or through vainglory, but in lowliness of mind each counting other better than himself;4 not looking each of you to his own things, but each of you also to the things of others.5 Have this mind in you, which was also in Christ Jesus:6 who, existing in the form of God, counted not the being on an equality with God a thing to be grasped,7 but emptied himself, taking the form of a servant, being made in the likeness of men;8 and being found in fashion as a man, he humbled himself, becoming obedient even unto death, yea, the death of the cross.9 Wherefore also God highly exalted him, and gave unto him the name which is above every name;10 that in the name of Jesus every knee should bow, of things in heaven and things on earth and things under the earth,11 and that every tongue should confess that Jesus Christ is Lord, to the glory of God the Father.12 So then, my beloved, even as ye have always obeyed, not as in my presence only, but now much more in my absence, work out your own salvation with fear and trembling;13 for it is God who worketh in you both to will and to work, for his good pleasure.14 Do all things without murmurings and questionings:15 that ye may become blameless and harmless, children of God without blemish in the midst of a crooked and perverse generation, among whom ye are seen as lights in the world,16 holding forth the word of life; that I may have whereof to glory in the day of Christ, that I did not run in vain neither labor in vain.17 Yea, and if I am offered upon the sacrifice and service of your faith, I joy, and rejoice with you all:18 and in the same manner do ye also joy, and rejoice with me.19 But I hope in the Lord Jesus to send Timothy shortly unto you, that I also may be of good comfort, when I know your state.20 For I have no man likeminded, who will care truly for your state.21 For they all seek their own, not the things of Jesus Christ.22 But ye know the proof of him, that, as a child serveth a father, so he served with me in furtherance of the gospel.23 Him therefore I hope to send forthwith, so soon as I shall see how it will go with me:24 but I trust in the Lord that I myself also shall come shortly.25 But I counted it necessary to send to you Epaphroditus, my brother and fellow-worker and fellow-soldier, and your messenger and minister to my need;26 since he longed after you all, and was sore troubled, because ye had heard that he was sick:27 for indeed he was sick nigh unto death: but God had mercy on him; and not on him only, but on me also, that I might not have sorrow upon sorrow.28 I have sent him therefore the more diligently, that, when ye see him again, ye may rejoice, and that I may be the less sorrowful.29 Receive him therefore in the Lord with all joy; and hold such in honor:30 because for the work of Christ he came nigh unto death, hazarding his life to supply that which was lacking in your service toward me.