previous next

FILIB 3

Adalci Mai Gaskiya

1 A ƙarshe kuma 'yan'uwa, ku yi farin ciki da Ubangiji. Sāke rubuto muku waɗannan abubuwa bai gundure ni ba, ga shi kuwa, domin lafiyarku ne.
2  t Ku yi hankali da karnukan nan! Ku yi hankali da mugayen ma'aikatan nan! Ku yi hankali da masu yankan jikin nan! 3 t Don mu ne masu kaciyar ainihi, masu bauta wa Allah ta wurin Ruhu, masu taƙama da Almasihu Yesu, ba mu kuma dogara da al'amuran ganin ido, 4 ko da yake ni ina iya dogara da al'amuran ganin ido, in dai nake so. In kuma akwai wanda yake tsammani yana iya dogara ga al'amuran ganin ido, to, ni na fi shi. 5 t An yi mini kaciya a rana ta takwas, asalina Isra'ila ne, na kabilar Biliyaminu, Ba'ibrane ɗan Ibraniyawa, bisa ga Shari'a kuwa ni Bafarisiye ne,

6 t a wajen himma kuwa mai tsananta wa Ikkilisiya ne ni, wajen aikin adalci kuwa bisa ga tafarkin Shari'a, marar abin zargi nake.
7  t Amma dai kowace irin riba na taɓa ci, na ɗauka hasara ce saboda Almasihu. 8 t Dahir na ɗauki dukkan abubuwa hasara ne, a kan mafificiyar darajar sanin da nake yi na Almasihu Yesu Ubangijina. Saboda shi ne na zaɓi yin hasarar dukkan abubuwa, har ma na mai da su tozari domin Almasihu yă zama nawa, 9 t a kuma same ni a cikinsa, ba da wani adalcin kaina ba, wanda ya danganta da bin Shari'a, sai dai da adalcin nan wanda yake tsirowa daga bangaskiya ga Almasihu, wato, da adalcin nan wanda yake samuwa daga Allah ta wurin bangaskiya. 10 t Muradina ke nan, in san Almasihu, in san ikon tashinsa daga matattu, in yi tarayya da shi a shan wuyarsa, in kuma zama kamarsa a wajen mutuwarsa,

11 t domin ta ko ƙaƙa in kai ga tashin nan daga matattu.

Nacewa Gaba Gaba zuwa Manufar


12  t Ba cewa, na riga na kai ga waɗannan ba ne, ko kuwa na zama kammalalle, a'a. sai dai ina nacewa ne, in riƙi abin nan da Almasihu Yesu ma ya riƙe ni saboda shi. 13 t Ya 'yan'uwa, ban ɗauka a kan cewa na riga na riƙi abin ba, amma abu guda kam ina yi, ina mantawa da abin da yake baya, ina kutsawa zuwa ga abin da yake gaba. 14 t Ina nacewa gaba gaba zuwa manufar nan, domin in sami ladar kiran nan zuwa sama, da Allah ya yi mini ta wurin Almasihu Yesu. 15 t Saboda haka ɗaukacin waɗanda suka kammala a cikinmu, sai su bi wannan ra'ayi. In kuwa a game da wani abu ra'ayinku ya sha bambam, to, Allah zai bayyana muku wannan kuma.

16 Sai dai a duk inda muka kai, mu ci gaba da haka.
17  t Ya ku 'yan'uwa, ku yi koyi da ni dukanku baki ɗaya, ku kuma dubi waɗanda zamansu yake daidai da gurbin da muka bar muku. 18 t Domin da yawa waɗanda na sha gaya muku, yanzu kuma nake gaya muku, har da hawaye, suna bin Yesu, in ji su, amma su magabtan gicciyen Almasihu ne. 19 t Ƙarshensu hallaka ne, Allahnsu ciki ne, rashin kunyarsu ita ce abar taƙamarsu, sun ƙwallafa ransu a kan al'amuran duniya. 20 t Mu kuwa 'yan Mulkin Sama ne, daga can ne kuma muke ɗokin zuwan Mai Ceto, Ubangiji Yesu Almasihu, 21 t wanda zai sāke jikin nan namu na ƙasƙanci, ya mai da shi kamar jikin nan nasa na ɗaukaka, da ikon nan nasa na sarayar da dukkan abubuwa a gare shi.

Philippians 3

1 Finally, my brethren, rejoice in the Lord. To write the same things to you, to me indeed is not irksome, but for you it is safe.2 Beware of the dogs, beware of the evil workers, beware of the concision:3 for we are the circumcision, who worship by the Spirit of God, and glory in Christ Jesus, and have no confidence in the flesh:4 though I myself might have confidence even in the flesh: if any other man thinketh to have confidence in the flesh, I yet more:5 circumcised the eighth day, of the stock of Israel, of the tribe of Benjamin, a Hebrew of Hebrews; as touching the law, a Pharisee;6 as touching zeal, persecuting the church; as touching the righteousness which is in the law, found blameless.7 Howbeit what things were gain to me, these have I counted loss for Christ.8 Yea verily, and I count all things to be loss for the excellency of the knowledge of Christ Jesus my Lord: for whom I suffered the loss of all things, and do count them but refuse, that I may gain Christ,9 and be found in him, not having a righteousness of mine own, even that which is of the law, but that which is through faith in Christ, the righteousness which is from God by faith:10 that I may know him, and the power of his resurrection, and the fellowship of his sufferings, becoming conformed unto his death;11 if by any means I may attain unto the resurrection from the dead.12 Not that I have already obtained, or am already made perfect: but I press on, if so be that I may lay hold on that for which also I was laid hold on by Christ Jesus.13 Brethren, I could not myself yet to have laid hold: but one thing I do, forgetting the things which are behind, and stretching forward to the things which are before,14 I press on toward the goal unto the prize of the high calling of God in Christ Jesus.15 Let us therefore, as many as are perfect, be thus minded: and if in anything ye are otherwise minded, this also shall God reveal unto you:16 only, whereunto we have attained, by that same rule let us walk.17 Brethren, be ye imitators together of me, and mark them that so walk even as ye have us for an ensample.18 For many walk, of whom I told you often, and now tell you even weeping, that they are the enemies of the cross of Christ:19 whose end is perdition, whose god is the belly, and whose glory is in their shame, who mind earthly things.20 For our citizenship is in heaven; whence also we wait for a Saviour, the Lord Jesus Christ:21 who shall fashion anew the body of our humiliation, that it may be conformed to the body of his glory, according to the working whereby he is able even to subject all things unto himself.