previous next

FILIB 4

Ku Yi Farin Ciki da Ubangiji

1  t Saboda haka ya 'yan'uwana, ƙaunatattuna, waɗanda nake bege, ku da kuke abin farin cikina da abin taƙamata kuma, ku dage ga Ubangiji, ya ku ƙaunatattuna.
2  t Na gargaɗi Afodiya, na kuma gargaɗi Sintiki, su yi zaman lafiya da juna saboda su na Ubangiji ne.

3 Ya kai abokin bautata na hakika, ina roƙonka, ka taimaki matan nan, don sun yi fama tare da ni a al'amarin bishara, haka ma Kilemas da sauran abokan aikina, waɗanda sunayensu suke a rubuce a cikin Littafin Rai.
4  t A kullum ku yi farin ciki da Ubangiji, har wa yau ina dai ƙara gaya muku, ku yi farin ciki. 5 t Bari kowa ya san jimirinku. Ubangiji ya yi kusan zuwa. 6 t Kada ku damu da kome, sai dai a kowane hali ku sanar da Allah bukatunku, ta wurin yin addu'a da roƙo, tare da gode wa Allah.

7 t Ta haka salamar Allah, wadda ta fi gaban dukkan fahimta, za ta tsai da zukatanku da tunaninku ga Almasihu Yesu.

Ku Yi Tunanin Waɗannan Abubuwa


8 Daga ƙarshe kuma, 'yan'uwa, ko mene ne yake na gaskiya, ko mene ne abin girmamawa, ko mene ne daidai, ko mene ne tsattsarka, ko mene ne abin ƙauna, ko mene ne daɗɗaɗar magana, in ma da wani abu mafifici, ko abin da ya cancanci yabo, a kan waɗannan abubuwa za ku yi tunani.

9 t Abin da kuka koya, kuka yi na'am da shi, abin kuma da kuka ji kuka gani a gare ni, sai ku aikata. Ta haka Allah mai zartar da salama zai kasance tare da ku.

Tabbatarwa da Kyautar da Filibiyawa Suka Aika


10  t Na yi farin ciki da Ubangiji ƙwarai da yake a yanzu kam, kularku gare ni ta farfaɗo, ko dā ma kuna kula da ni, dama ce ba ku samu ba. 11 t Ba cewa, ina kukan rashi ba ne, domin na koyi yadda zan zauna da wadar zuci a cikin kowane irin hali da nake. 12 t Na san yadda zan yi in yi zaman ƙunci, na kuma san yadda zan yi in yi zaman yalwa. A kowane irin hali duka na horu da ƙoshi da yunwa, yalwa da rashi.

13 t Zan iya yin kome albarkacin wannan da yake ƙarfafa ni.
14  t Amma kuwa kun kyauta da kuka taya ni cikin ƙuntatata. 15 t Ku kuma Filibiyawa, ku kanku kun sani tun da aka fara yin bishara, sa'ad da na bar ƙasar Makidoniya, ba wata ikkilisiyar da ta yi tarayya da ni wajen hidimar bayarwa da karɓa, sai dai ku kaɗai. 16 t Ko sa'ad da nake Tasalonika ma, kun aiko mini da taimako ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba. 17 t Ba cewa, don ina neman kyautarku ba ne, a'a, nemar muku amfani nake yi, a ƙara a kan ribarku. 18 t An biya ni sarai, har fi. Bukatata ta biya, da na karɓi kyautar da kuka aiko mini ta hannun Abafaroditas, baiwa mai ƙanshi, hadaya abar karɓa, mai faranta wa Allah rai. 19 t Allahna kuma zai biya muku kowace bukatarku daga cikin yalwar ɗaukakarsa da take ga Almasihu Yesu.

20 t Ɗaukaka tā tabbata ga Allahnmu, Ubanmu, har abada abadin. Amin! Amin!

Gaisuwa


21  t Ku gai da kowane tsattsarka cikin Almasihu Yesu. 'Yan'uwan da suke tare da ni suna gai da ku.

22 t Dukan tsarkaka suna gai da ku, tun ba ma na fadar Kaisar ba.
23  t Alherin Ubangiji Yesu Almasihu yă tabbata a zukatanku.

Philippians 4

1 Wherefore, my brethren beloved and longed for, my joy and crown, so stand fast in the Lord, my beloved.2 I exhort Euodia, and I exhort Syntyche, to be of the same mind in the Lord.3 Yea, I beseech thee also, true yokefellow, help these women, for they labored with me in the gospel, with Clement also, and the rest of my fellow-workers, whose names are in the book of life.4 Rejoice in the Lord always: again I will say, Rejoice.5 Let your forbearance be known unto all men. The Lord is at hand.6 In nothing be anxious; but in everything by prayer and supplication with thanksgiving let your requests be made known unto God.7 And the peace of God, which passeth all understanding, shall guard your hearts and your thoughts in Christ Jesus.8 Finally, brethren, whatsoever things are true, whatsoever things are honorable, whatsoever things are just, whatsoever things are pure, whatsoever things are lovely, whatsoever things are of good report; if there be any virtue, and if there be any praise, think on these things.9 The things which ye both learned and received and heard and saw in me, these things do: and the God of peace shall be with you.10 But I rejoice in the Lord greatly, that now at length ye have revived your thought for me; wherein ye did indeed take thought, but ye lacked opportunity.11 Not that I speak in respect of want: for I have learned, in whatsoever state I am, therein to be content.12 I know how to be abased, and I know also how to abound: in everything and in all things have I learned the secret both to be filled and to be hungry, both to abound and to be in want.13 I can do all things in him that strengtheneth me.14 Howbeit ye did well that ye had fellowship with my affliction.15 And ye yourselves also know, ye Philippians, that in the beginning of the gospel, when I departed from Macedonia, no church had fellowship with me in the matter of giving and receiving but ye only;16 for even in Thessalonica ye sent once and again unto my need.17 Not that I seek for the gift; but I seek for the fruit that increaseth to your account.18 But I have all things, and abound: I am filled, having received from Epaphroditus the things that came from you, and odor of a sweet smell, a sacrifice acceptable, well-pleasing to God.19 And my God shall supply every need of yours according to his riches in glory in Christ Jesus.20 Now unto our God and Father be the glory for ever and ever. Amen.21 Salute every saint in Christ Jesus. The brethren that are with me salute you.22 All the saints salute you, especially they that are of Caesar’s household.23 The grace of the Lord Jesus Christ be with your spirit.