W. YAH 12
Wata Mace da Macijin
1 Aka kuma ga wata babbar alama a sama, wata mace tana a lulluɓe da rana, tana a tsaye a kan wata, da kuma kambi mai taurari goma sha biyu a kanta. 2 t Tana da ciki, sai kuma ta yi ta ƙara ta ƙagauta domin ta haihu, saboda azabar naƙuda. 3 t Sai kuma aka ga wata alama a sama, ga wani ƙaton jan maciji mai kawuna bakwai, da ƙahoni goma, da kambi bakwai a kawunansa. 4 t Wutsiyarsa ta sharo sulusin taurari, ta zuba su a ƙasa. Sai macijin ya tsaya a gaban matar nan mai naƙuda, don ya lanƙwame ɗan nata in ta haife shi. 5 t Ta kuwa haifi ɗa namiji, wanda zai mallaki dukkan al'ummai da sandar ƙarfe, amma aka fyauce ɗan nata, aka kai shi zuwa wurin Allah da kursiyinsa.
6 t Matar kuwa, sai ta gudu ta shiga jeji, a inda Allah ya shirya mata wurin da za a cishe ta har kwana dubu da metan da sittin.
7 t Sai yaƙi ya tashi a sama, Mika'ilu da mala'ikunsa suna yaƙi da macijin nan, macijin kuma da mala'ikunsa suka yi ta yaƙi, 8 amma aka cinye su, har suka rasa wuri a sama sam. 9 t Sai aka jefa ƙaton macijin nan a ƙasa, wato macijin nan na tun dā dā, wanda ake kira Ibilis da Shaiɗan, mayaudarin dukkan duniya, aka jefa shi a duniya, mala'ikunsa ma aka jefa su tare da shi. 10 t Sai na ji wata murya mai ƙara a Sama tana cewa, “A yanzu fa, ceto, da ƙarfi, da mulki na Allahnmu, da kuma ikon Almasihunsa sun bayyana, don an jefa mai ƙarar 'yan'uwanmu a ƙasa, shi da yake ƙararsu dare da rana a gun Allahnmu. 11 t Sun kuwa yi nasara da shi albarkacin jinin Ɗan Ragon nan, da kuma albarkacin maganar da suka shaida, domin ba su yi tattalin ransu ba, har abin ya kai su ga kisa.
12 t Saboda haka, sai ku yi farin ciki, ya ku sammai, da ku mazauna a ciki. Amma kaitonku, ke ƙasa, da kai teku, don Ibilis ya sauko gare ku da matsanancin fushi, don ya san lokacinsa ya ƙure.”
13 t Da macijin nan ya ga an jefa shi a ƙasa, ya fafari matar nan da ta haifi ɗa namiji, da tsanani. 14 t Amma aka ba matar fikafikan nan biyu na babban juhurman nan, don ta tashi ta guje wa macijin nan, ta shiga jeji, ta je wurin da za a cishe ta a lokaci ɗaya, da lokatai, da rabin lokaci. 15 Sai macijin ya kwarara ruwa daga bakinsa kamar kogi daga bayan matar, don ya share ta da ambaliya. 16 Amma ƙasa ta taimaki matar, ita ƙasar ta buɗe bakinta ta shanye kogin da macijin nan ya kwararo daga bakinsa. 17 t Macijin kuwa ya yi fushi da matar, ya tafi ya ɗaura yaƙi da sauran zuriyarta, wato, waɗanda suke kiyaye umarnin Allah, suke kuma shaidar Yesu. Sai ya tsaya a kan yashin teku.
Revelation 12
1 And a great sign was seen in heaven: a woman arrayed with the sun, and the moon under her feet, and upon her head a crown of twelve stars;2 and she was the child; and she crieth out, travailing in birth, and in pain to be delivered.3 And there was seen another sign in heaven: and behold, a great red dragon, having seven heads and ten horns, and upon his heads seven diadems.4 And his tail draweth the third part of the stars of heaven, and did cast them to the earth: and the dragon standeth before the woman that is about to be delivered, that when she is delivered he may devour her child.5 And she was delivered of a son, a man child, who is to rule all the nations with a rod of iron: and her child was caught up unto God, and unto his throne.6 And the woman fled into the wilderness, where she hath a place prepared of God, that there they may nourish her a thousand two hundred and threescore days.7 And there was war in heaven: Michael and his angels going forth to war with the dragon; and the dragon warred and his angels;8 And they prevailed not, neither was their place found any more in heaven.9 And the great dragon was cast down, the old serpent, he that is called the Devil and Satan, the deceiver of the whole world; he was cast down to the earth, and his angels were cast down with him.10 And I heard a great voice in heaven, saying, Now is come the salvation, and the power, and the kingdom of our God, and the authority of his Christ: for the accuser of our brethren is cast down, who accuseth them before our God day and night.11 And they overcame him because of the blood of the Lamb, and because of the word of their testimony; and they loved not their life even unto death.12 Therefore rejoice, O heavens, and ye that dwell in them. Woe for the earth and for the sea: because the devil is gone down unto you, having great wrath, knowing that he hath but a short time.
13 And when the dragon saw that he was cast down to the earth, he persecuted the woman that brought forth the man child.14 And there were given to the woman the two wings of the great eagle, that she might fly into the wilderness unto her place, where she is nourished for a time, and times, and half a time, from the face of the serpent.15 And the serpent cast out of his mouth after the woman water as a river, that he might cause her to be carried away by the stream.16 And the earth helped the woman, and the earth opened her mouth and swallowed up the river which the dragon cast out of his mouth.17 And the dragon waxed wroth with the woman, and went away to make war with the rest of her seed, that keep the commandments of God, and hold the testimony of Jesus: