previous next

W. YAH 16

Tasoshin Azaba

1  t Sai na ji wata murya mai ƙara daga Haikalin, tana ce wa mala'ikun nan bakwai, “Ku je ku juye tasoshin nan bakwai na fushin Allah a kan duniya.”

2  t Daga nan mala'ikan farko ya je ya juye abin da yake a tasarsa a kan duniya, sai kuwa waɗansu mugayen miyaku masu azabtarwa suka fito a jikin mutanen da suke da alamar dabbar nan, suke kuma yi wa siffarta sujada.

3  t Mala'ika na biyu ya juye abin da yake a tasarsa a teku, ya zama kamar jinin mataccen mutum, kowane abu mai rai na cikin teku kuma ya mutu.
4  t Mala'ika na uku ya juye abin da yake a tasarsa a koguna da maɓuɓɓugan ruwa, sai suka zama jini.

5 t Na kuwa ji mala'ikan ruwa yana cewa,
“Kai mai adalci ne a hukuncin nan naka,
Ya kai Mai Tsarki, wanda kake a yanzu, kake kuma a dā.

6  t Don mutane sun zub da jinin tsarkaka da na annabawa,
Ga shi kuwa, ka ba su jini su sha.
Sakamakonsu ke nan!”

7  t Sai na ji wata murya a bagadin ƙona turare, tana cewa,
“Hakika, ya Ubangiji Allah Maɗaukaki,
Hukuncinka daidai yake, na adalci ne kuma!”
8  t Sai mala'ika na huɗu ya juye abin da yake a tasarsa a rana, sai aka yardar mata ta ƙona mutane da wuta.

9 t Sai matsanancin zafi ya ƙona mutane, har suka zagi sunan Allah, shi da yake da ikon waɗannan bala'i, ba su kuwa tuba sun ɗaukaka shi ba.
10  t Mala'ika na biyar ya juye abin da yake a tasarsa a kursiyin dabbar nan, sai mulkinta ya zama duhu, har mutane suka ciji leɓunansu don azaba,

11 t suka zagi Allah Mai Sama saboda azabarsu da miyakunsu, ba su kuma tuba da ayyukansu ba.
12  t Mala'ika na shida ya juye abin da yake a tasarsa a babban kogin nan Yufiretis, sai ruwansa ya ƙafe, don a shirya wa sarakuna daga gabas tafarki. 13 t Na kuma ga baƙaƙen aljannu masu kama da kwaɗi gudu uku, suna fitowa daga bakin macijin nan, da bakin dabbar nan, da kuma bakin annabin nan na ƙarya, 14 t su iskoki ne, aljannu masu yin abubuwan al'ajabi, masu zuwa wurin sarakunan duniya duka, don su tara su saboda yaƙi a babbar ranar nan ta Allah Maɗaukaki. 15 t (“Ga ni nan a tafe kamar ɓarawo! Albarka tā tabbata ga wanda yake a zaune a faɗake, yana saye da tufafinsa, don kada ya tafi tsirara, a ga tsiraicinsa.”)

16 t Sai suka tattara su a wurin da ake kira Armageddon da Yahudanci.
17  t Mala'ika na bakwai ya juye abin da yake a tasarsa a sararin sama, sai aka ji wata murya mai ƙara daga Haikali, wato, daga kursiyin, ta ce, “An gama!” 18 t Sai aka yi ta walƙiya, da ƙararraki masu tsanani, da aradu, da wata babbar rawar ƙasa irin wadda ba a taɓa yi ba, tun da ɗan adam yake a duniya, gawurtacciyar rawar ƙasa ƙwarai da gaske. 19 t Babban birnin nan kuwa ya rabu gida uku, biranen al'ummai kuma suka fāɗi. Sai Allah ya tuna da Babila mai girma, don ya sa ta, ta sha fushinsa mai tsananin gaske. 20 t Kowane tsibiri ya ɓace, manyan duwatsu ma ba a ƙara ganinsu ba. 21 t Waɗansu manyan ƙanƙara kuma kamar kayan jaki suka faɗo a kan mutane daga sama, har mutane suka zagi Allah, saboda bala'in ƙanƙarar. Bala'in nan da matuƙar bantsoro yake!

Revelation 16

1 And I heard a great voice out of the temple, saying to the seven angels, Go ye, and pour out the seven bowls of the wrath of God into the earth.2 And the first went, and poured out his bowl into the earth; and it became a noisome and grievous sore upon the men that had the mark of the beast, and that worshipped his image.3 And the second poured out his bowl into the sea; and it became blood as of a dead man; and every living soul died, even the things that were in the sea.4 And the third poured out his bowl into the rivers and the fountains of the waters; and it became blood.5 And I heard the angel of the waters saying, Righteous art thou, who art and who wast, thou Holy One, because thou didst thus judge:6 for they poured out the blood of the saints and the prophets, and blood hast thou given them to drink: they are worthy.7 And I heard the altar saying, Yea, O Lord God, the Almighty, true and righteous are thy judgments.8 And the fourth poured out his bowl upon the sun; and it was given unto it to scorch men with fire.9 And men were scorched men with great heat: and they blasphemed the name of God who hath the power over these plagues; and they repented not to give him glory.10 And the fifth poured out his bowl upon the throne of the beast; and his kingdom was darkened; and they gnawed their tongues for pain,11 and they blasphemed the God of heaven because of their pains and their sores; and they repented not of their works.12 And the sixth poured out his bowl upon the great river, the river Euphrates; and the water thereof was dried up, that the way might by made ready for the kings that come from the sunrising.13 And I saw coming out of the mouth of the dragon, and out of the mouth of the beast, and out of the mouth of the false prophet, three unclean spirits, as it were frogs:14 for they are spirits of demons, working signs; which go forth unto the kings of the whole world, to gather them together unto the war of the great day of God, the Almighty.15 (Behold, I come as a thief. Blessed is he that watcheth, and keepeth his garments, lest he walked naked, and they see his shame.)16 And they gathered them together into the place which is called in Hebrew Har-magedon.17 And the seventh poured out his bowl upon the air; and there came forth a great voice out of the temple, from the throne, saying, It is done:18 and there were lightnings, and voices, and thunders; and there was a great earthquake, such as was not since there were men upon the earth, so great an earthquake, so mighty.19 And the great city was divided into three parts, and the cities of the nations fell: and Babylon the great was remembered in the sight of God, to give unto her the cup of the wine of the fierceness of his wrath.20 And every island fled away, and the mountains were not found.21 And great hail, every stone about the weight of a talent, cometh down out of heaven upon men: and men blasphemed God because of the plague of the hail; for the plague thereof is exceeding great.