W. YAH 20
Shekara Dubu
1 t Sa'an nan na ga wani mala'ika yana saukowa daga Sama, yana a riƙe da mabuɗin mahallaka, da kuma wata babbar sarƙa a hannunsa. 2 t Sai ya kama macijin nan, wato, macijin nan na tun dā dā, wanda yake shi ne Ibilis, shi ne kuma Shaiɗan, ya ɗaure shi har shekara dubu,
3 t ya jefa shi mahallakar, ya rufe, ya kuma yimƙe ta da hatimi, don kada ya ƙara yaudarar al'ummai, har dai shekarun nan dubu su ƙare. Bayan wannan lalle ne a sake shi zuwa ɗan lokaci kaɗan.
4 t Sa'an nan na ga kursiyai, da waɗanda aka bai wa ikon hukunci, zaune a kai. Har wa yau, kuma na ga rayukan waɗanda aka fille wa kai saboda shaidar da suka yi wa Yesu, da kuma Maganar Allah, ba su kuwa yi wa dabbar nan da siffarta sujada ba, ba su kuma yarda a yi musu alamarta a goshinsu ko a hannunsu ba, sun sāke rayuwa, sun yi mulki tare da Almasihu har shekara dubu. 5 t Sauran matattu kuwa, ba su sāke rayuwa ba, sai bayan da shekaran nan dubu suka cika. Wannan fa shi ne tashin matattu na farko.
6 t Duk wanda yake da rabo a tashin nan na farko, mai albarka ne, tsattsarka ne. Mutuwa ta biyu ba ta da iko a kan irin waɗannan, amma za su zama firistocin Allah da na Almasihu, su kuma yi mulki tare da shi har shekara dubu.
7 t Bayan shekaran nan dubu sun ƙare, sai a saki Shaiɗan daga ɗaurinsa, 8 t ya kuma fito ya yaudari al'ummai waɗanda suke kusurwoyin nan huɗu na duniya, wato, Gog da Magog, ya tattara su saboda yaƙi, yawansu kamar yashin teku. 9 t Sai kuma su bazu, su mamaye duk duniya, su yi wa sansanin tsarkaka da ƙaunataccen birni ƙawanya, sai wuta ta zubo daga sama ta lashe su.
10 t Shi kuwa Ibilis mayaudarinsu, sai da aka jefa shi a tafkin wuta da ƙibiritu, a inda dabbar nan da annabin nan na ƙarya suke, za a kuma gwada musu azaba dare da rana har abada abadin.Ranar Shari'a a Gaban Babban Farin Kursiyi
11 t Sa'an nan na ga wani babban kursiyi fari, da wanda yake a zaune a kai, sai sama da ƙasa suka guje wa Zatinsa, suka ɓace. 12 t Sai na ga matattu manya da yara, a tsaitsaye a gaban kursiyin, aka kuma buɗe littattafai. Sai kuma aka buɗe wani littafi, wanda yake shi ne Littafin Rai. Aka kuwa yi wa matattu shari'a bisa ga abin da yake a rubuce a cikin littattafan, gwargwadon aikin da suka yi. 13 t Sai teku ta ba da matattun da suke a cikinta, mutuwa da Hades kuma sun ba da matattun da suke a gare su, aka kuwa yi wa kowa shari'a gwargwadon aikin da ya yi. 14 t Sa'an nan aka jefa mutuwa da Hades a tafkin nan na wuta. Wannan ita ce mutuwa ta biyu, wato, tafkin wuta. 15 t Duk wanda ba a sami sunansa a rubuce a Littafin Rai ba, sai a jefa shi a tafkin nan na wuta.
Revelation 20
1 And I saw an angel coming down out of heaven, having the key of the abyss and a great chain in his hand.2 And he laid hold on the dragon, the old serpent, which is the Devil and Satan, and bound him for a thousand years,3 and cast him into the abyss, and shut it, and sealed it over him, that he should deceive the nations no more, until the thousand years should be finished: after this he must be loosed for a little time.4 And I saw thrones, and they sat upon them, and judgment was given unto them: and I saw the souls of them that had been beheaded for the testimony of Jesus, and for the word of God, and such as worshipped not the beast, neither his image, and received not the mark upon their forehead and upon their hand; and they lived, and reigned with Christ a thousand years.5 The rest of the dead lived not until the thousand years should be finished. This is the first resurrection.6 Blessed and holy is he that hath part in the first resurrection: over these the second death hath no power; but they shall be priests of God and of Christ, and shall reign with him a thousand years.7 And when the thousand years are finished, Satan shall be loosed out of his prison,8 and shall come forth to deceive the nations which are in the four corners of the earth, Gog and Magog, to gather them together to the war: the number of whom is as the sand of the sea.9 And they went up over the breadth of the earth, and compassed the camp of the saints about, and the beloved city: and fire came down out of heaven, and devoured them.10 And the devil that deceived them was cast into the lake of fire and brimstone, where are also the beast and the false prophet; and they shall be tormented day and night for ever and ever.11 And I saw a great white throne, and him that sat upon it, from whose face the earth and the heaven fled away; and there was found no place for them.12 And I saw the dead, the great and the small, standing before the throne; and books were opened: and another book was opened, which is the book of life: and the dead were judged out of the things which were written in the books, according to their works.13 And the sea gave up the dead that were in it; and death and Hades gave up the dead that were in them: and they were judged every man according to their works.14 And death and Hades were cast into the lake of fire. This is the second death, even the lake of fire.15 And if any was not found written in the book of life, he was cast into the lake of fire.