W. YAH 21
Sabuwar Sama da Sabuwar Ƙasa
1 t Sa'an nan na ga sabuwar sama da sabuwar ƙasa, don sama ta farko da ƙasa ta farko sun shuɗe, ba kuma sauran teku. 2 t Sai na ga tsattsarkan birni kuma, Sabuwar Urushalima, tana saukowa daga Sama daga wurin Allah, shiryayyiya kamar amaryar da ta yi ado saboda mijinta. 3 t Na kuma ji wata murya mai ƙara daga kursiyin, tana cewa, “Kun ga, mazaunin Allah na tare da mutane. Zai zauna tare da su, za su zama jama'arsa, Allah kuma shi kansa zai kasance tare da su,
4 t zai share musu dukkan hawaye. Ba kuma sauran mutuwa, ko baƙin ciki, ko kuka, ko azaba, don abubuwan dā sun wuce.”
5 t Sai na zaune a kan kursiyin ya ce, “Kun ga, ina yin kome sabo.” Ya kuma ce, “Rubuta wannan, domin maganar nan tabbatacciya ce, gaskiya ce kuma.” 6 t Sai ya ce mini, “An gama! Ni ne Alfa, Ni ne Omega, Ni ne na Farko, Ni ne kuma na Ƙarshe. Duk mai jin ƙishirwa zan ba shi ruwa daga maɓuɓɓugar ruwan rai kyauta. 7 Duk wanda ya ci nasara, zai ci wannan gādo, wato, in zama Allahnsa, shi kuma ya zama ɗa a gare ni.
8 t Amma matsorata, da marasa riƙon amana, da masu aikin ƙyama, da masu kisankai, da fasikai, da masu sihiri, da masu bautar gumaka, da kuma duk maƙaryata, duk rabonsu tafkin nan ne mai cin wuta da kibiritu, wanda yake shi ne mutuwa ta biyu.”Sabuwar Urushalima
9 t Sai kuma ɗaya daga cikin mala'ikun nan bakwai, masu tasoshin nan bakwai, cike da bala'i bakwai na ƙarshe, ya zo ya yi mini magana, ya ce, “Zo in nuna maka amarya, matar Ɗan Ragon.” 10 t Sai ya ɗauke ni, Ruhu yana iza ni, ya kai ni wani babban dutse mai tsawo, ya nuna mini tsattsarkan birnin Urushalima yana saukowa daga Sama daga wurin Allah, 11 t yana tare da ɗaukakar Allah. Hasken birnin yana ƙyalƙyali kamar wani irin nadirin dutse mai daraja, kamar yasfa, garau kamar ƙarau. 12 t Yana da babban garu mai tsawo, da ƙofar gari goma sha biyu, a ƙofofi ɗin da akwai mala'iku goma sha biyu. A jikin ƙofofin kuma an rubuta sunayen kabilan nan goma sha biyu na Isra'ila, 13 a gabas, ƙofa uku, a yamma ƙofa uku, a kudu ƙofa uku, a arewa kuma ƙofa uku.
14 Garun birnin kuwa, tana da dutsen harsashi goma sha biyu, a jikinsu kuma an rubuta sunayen manzannin nan goma sha biyu na Ɗan Ragon.
15 t Shi wanda ya yi mini magana kuwa yana da sandar awo ta zinariya, domin ya auna birnin, da ƙofofinsa, da garunsa. 16 Birnin murabba'i ne, tsawonsa da fāɗinsa duka ɗaya ne. Sai ya auna birnin da sandarsa, mil dubu da ɗari biyar, tsawonsa, da fāɗinsa da zacinsa, duka ɗaya suke. 17 Ya kuma auna garunsa, kamu ɗari da arba'in da huɗu ne na mutum, wato, na mala'ika ke nan. 18 t Garun kuwa da yasfa aka gina shi, birnin kuma da zinariya zalla, garau kamar ƙarau. 19 t An kuma ƙawata harsasan garun birnin da kowane irin dutse mai daraja. Yasfa shi ne na farko, na biyu saffir, na uku agat, na huɗu zumurrudu, 20 t na biyar onis, na shida yaƙutu, na bakwai kirisolat, na takwas beril, na tara tofaz, na goma kirisofaras, na sha ɗaya yakinta, na sha biyu kuma ametis.
21 t Ƙofofin gari goma sha biyun nan kuwa lu'ulu'u ne goma sha biyun, kowace ƙofa da lu'ulu'u guda aka yi ta, hanyar birnin kuwa zinariya ce zalla garau kamar ƙarau.
22 t Ban kuwa ga wani Haikali a birnin ba, domin Haikalinsa Ubangiji Allah Maɗaukaki ne, da kuma Ɗan Ragon. 23 t Birnin kuwa ba ya bukatar rana ko wata su haskaka shi, domin ɗaukakar Allah ita ce haskensa, Ɗan Ragon kuma fitilarsa. 24 t Da haskensa al'ummai za su yi tafiya. Sarakunan duniya za su kawo darajarsu a gare shi. 25 t Ƙofofinsa kuwa ba za a rufe su da rana ba har abada, ba kuwa za a yi dare a can ba. 26 Za a kuma kawo darajar al'ummai da girmansu a gare shi. 27 t Amma ko kaɗan ba wani abu marar tsarki da zai shiga cikinsa, ko wani mai aikata abin ƙyama ko ƙarya, sai dai waɗanda aka rubuta sunayensu a Littafin Rai na Ɗan Ragon kaɗai.
Revelation 21
1 And I saw a new heaven and a new earth: for the first heaven and the first earth are passed away; and the sea is no more.2 And I saw the holy city, new Jerusalem, coming down out of heaven from God, made ready as a bride adorned for her husband.3 And I heard a great voice out of the throne saying, Behold, the tabernacle of God is with men, and he shall dwell with them, and they shall be his peoples, and God himself shall be with them, and be their God:4 and he shall wipe away every tear from their eyes; and death shall be no more; neither shall there be mourning, nor crying, nor pain, any more: the first things are passed away.5 And he that sitteth on the throne said, Behold, I make all things new. And he saith, Write: for these words are faithful and true.6 And he said unto me, They are come to pass. I am the Alpha and the Omega, the beginning and the end. I will give unto him that is athirst of the fountain of the water of life freely.7 He that overcometh shall inherit these things; and I will be his God, and he shall be my son.8 But for the fearful, and unbelieving, and abominable, and murderers, and fornicators, and sorcerers, and idolaters, and all liars, their part shall be in the lake that burneth with fire and brimstone; which is the second death.9 And there came one of the seven angels who had the seven bowls, who were laden with the seven last plagues; and he spake with me, saying, Come hither, I will show thee the bride, the wife of the Lamb.10 And he carried me away in the Spirit to a mountain great and high, and showed me the holy city Jerusalem, coming down out of heaven from God,11 having the glory of God: her light was like unto a stone most precious, as it were a jasper stone, clear as crystal:12 having a wall great and high; having twelve gates, and at the gates twelve angels; and names written thereon, which are the names of the twelve tribes of the children of Israel:13 on the east were three gates; and on the north three gates; and on the south three gates; and on the west three gates.14 And the wall of the city had twelve foundations, and on them twelve names of the twelve apostles of the Lamb.15 And he that spake with me had for a measure a golden reed to measure the city, and the gates thereof, and the wall thereof.16 And the city lieth foursquare, and the length thereof is as great as the breadth: and he measured the city with the reed, twelve thousand furlongs: the length and the breadth and the height thereof are equal.17 And he measured the wall thereof, a hundred and forty and four cubits, according to the measure of a man, that is, of an angel.18 And the building of the wall thereof was jasper: and the city was pure gold, like unto pure glass.19 The foundations of the wall of the city were adorned with all manner of precious stones. The first foundation was jasper; the second, sapphire; the third, chalcedony; the fourth, emerald;20 the fifth, sardonyx; the sixth, sardius; the seventh, chrysolite; the eighth, beryl; the ninth, topaz; the tenth, chrysoprase; the eleventh, jacinth; the twelfth, amethyst.21 And the twelve gates were twelve pearls; each one of the several gates was of one pearl: and the street of the city was pure gold, as it were transparent glass.22 And I saw no temple therein: for the Lord God the Almighty, and the Lamb, are the temple thereof.23 And the city hath no need of the sun, neither of the moon, to shine upon it: for the glory of God did lighten it, and the lamp thereof is the Lamb.24 And the nations shall walk amidst the light thereof: and the kings of the earth bring their glory into it.25 And the gates thereof shall in no wise be shut by day (for there shall be no night there):26 and they shall bring the glory and the honor of the nations into it:27 and there shall in no wise enter into it anything unclean, or he that maketh an abomination and a lie: but only they that are written in the Lamb’s book of life.