W. YAH 22
1 t Sa'an nan, sai ya nuna mini kogin ruwan rai, yana ƙyalli kamar ƙarau, yana gudana daga kursiyin Allah, shi da Ɗan Rago, 2 t ta tsakiyar hanyar birnin kuma, ta kowane gefen kogin, akwai itatuwan rai masu haihuwar 'ya'ya iri goma sha biyu, kowane wata suna haihuwa, ganyen itatuwan kuwa saboda lafiyar al'ummai ne. 3 t Ba sauran wani abin la'antarwa, amma kursiyin Allah, shi da Ɗan Rago, zai kasance a cikinsa. Bayinsa za su bauta masa, 4 t za su kuma ga fuskarsa, sunansa kuwa zai kasance a goshinsu.
5 t Ba za a ƙara yin dare ba, ba za su bukaci hasken fitila, ko na rana ba, domin Ubangiji Allah zai haskaka su, za su kuma sha ni'imar Mulki har abada abadin.Yesu Yana Zuwa da Wuri
6 t Sai ya ce mini, “Wannan magana tabbatacciya ce, ta gaskiya ce kuma. Ubangiji, Allahn ruhohin annabawa ya aiko mala'ikansa, ya nuna wa bayinsa abin da lalle ne zai auku ba da daɗewa ba.”
7 t “Ga shi kuwa, ina zuwa da wuri. Albarka tā tabbata ga wanda yake kiyaye maganar annabcin littafin nan.”
8 t Ni Yahaya, ni ne na ji, na kuma ga waɗannan abubuwa. Sa'ad da kuwa na ji su, na kuma gan su, sai na fāɗi a gaban mala'ikan da ya nuna mini su, domin in yi masa sujada.
9 t Amma, sai ya ce mini, “Ko kusa kada ka yi haka! Ni abokin bautarku ne, kai da 'yan'uwanka annabawa, da kuma waɗanda suke kiyaye maganar littafin nan. Allah za ka yi wa sujada.”
10 t Ya kuma ce mini, “Kada ka rufe maganar annabcin littafin nan, domin lokaci ya kusa.
11 t Marar gaskiya yă yi ta rashin gaskiyarsa, fajiri kuwa yă yi ta fajircinsa, adali kuwa yă yi ta aikata adalcinsa, wanda yake tsattsarka kuwa ya yi ta zamansa na tsarki.”
12 t “Ga shi, ina zuwa da wuri, tare da sakamakon da zan yi wa kowa gwargwadon abin da ya yi.
13 t Ni ne Alfa, Ni ne Omega, Ni ne na Farko, Ni ne na Ƙarshe.”
14 t Albarka tā tabbata ga masu wanke rigunansu, domin su sami izinin ɗiba daga itacen rai, su kuma shiga birnin ta ƙofa.
15 t Waɗanda aka hana shiga birnin kuwa, su ne fajirai, da masu sihiri, da fasikai, da masu kisankai, da masu bautar gumaka, da kuma duk wanda yake son ƙarya, yake kuma yinta.
16 t “Ni Yesu, na aiko mala'ikana a gare ka, da wannan shaida saboda ikilisiyoyi. Ni ne tsatson Dawuda, da zuriyarsa, Gamzaki mai haske.”
17 t Ruhu da amarya suna cewa, “Zo.” Duk wanda ya ji kuwa, yă ce, “Zo.” Duk mai jin ƙishirwa ya zo, duk mai bukata, yă ɗibi ruwan rai kyauta.
18 t Ina yi wa duk mai jin maganar annabcin littafin nan kashedi, in wani ya yi wani ƙari a kanta, Allah zai ƙara masa bala'in da aka rubuta a littafin nan.
19 t In kuma wani ya yi ragi a maganar littafin annabcin nan, Allah zai ɗauke rabonsa na itacen rai, da na tsattsarkan birnin, waɗanda aka rubuta a littafin nan.
20 t Shi wanda ya shaida abubuwan nan ya ce, “Hakika, ina zuwa da wuri.” Amin! Zo, ya Ubangiji Yesu.
21 t Alherin Ubangiji Yesu yă tabbata ga dukkan tsarkaka. Amin!
Revelation 22
1 And he showed me a river of water of life, bright as crystal, proceeding out of the throne of God and of the Lamb,2 in the midst of the street thereof. And on this side of the river and on that was the tree of life, bearing twelve manner of fruits, yielding its fruit every month: and the leaves of the tree were for the healing of the nations.3 And there shall be no curse any more: and the throne of God and of the Lamb shall be therein: and his servants shall serve him;4 and they shall see his face; and his name shall be on their foreheads.5 And there shall be night no more; and they need no light of lamp, neither light of sun; for the Lord God shall give them light: and they shall reign for ever and ever.6 And he said unto me, These words are faithful and true: and the Lord, the God of the spirits of the prophets, sent his angels to show unto his servants the things which must shortly come to pass.7 And behold, I come quickly. Blessed is he that keepeth the words of the prophecy of this book.8 And I John am he that heard and saw these things. And when I heard and saw, I fell down to worship before the feet of the angel that showed me these things.9 And he saith unto me, See thou do it not: I am a fellow-servant with thee and with thy brethren the prophets, and with them that keep the words of this book: worship God.10 And he saith unto me, Seal not up the words of the prophecy of this book; for the time is at hand.11 He that is unrighteous, let him do unrighteousness still: and he that is filthy, let him be made filthy still: and he that is righteous, let him do righteousness still: and he that is holy, let him be made holy still.12 Behold, I come quickly; and my reward is with me, to render to each man according as his work is.13 I am the Alpha and the Omega, the first and the last, the beginning and the end.14 Blessed are they that wash their robes, that they may have the right to come to the tree of life, and may enter in by the gates into the city.15 Without are the dogs, and the sorcerers, and the fornicators, and the murderers, and the idolaters, and every one that loveth and maketh a lie.16 I Jesus have sent mine angel to testify unto you these things for the churches. I am the root and the offspring of David, the bright, the morning star.17 And the Spirit and the bride say, Come. And he that heareth, let him say, Come. And he that is athirst, let him come: he that will, let him take the water of life freely.18 I testify unto every man that heareth the words of the prophecy of this book, if any man shall add unto them, God shall add unto him the plagues which are written in this book:19 and if any man shall take away from the words of the book of this prophecy, God shall take away his part from the tree of life, and out of the holy city, which are written in this book.20 He who testifieth these things saith, Yea: I come quickly. Amen: come, Lord Jesus.21 The grace of the Lord Jesus be with the saints. Amen.