ROM 1
Gaisuwa
1 t Daga Bulus, bawan Yesu Almasihu, manzo kirayayye, keɓaɓɓe domin yin bisharar Allah, 2 t wadda Allah ya yi alkawari tun dā, ta bakin annabawansa a cikin Littattafai masu tsarki. 3 t Bishara ɗin nan a kan Ɗansa ce, Ubangijinmu Yesu Almasihu, wanda ga jiki shi zuriyar Dawuda ne, 4 amma ga tsarkinsa na ruhu shi Ɗan Allah ne, da iko aka ayyana shi haka ta wurin tashinsa daga matattu. 5 t Ta wurinsa ne muka sami alheri da kuma manzanci, saboda sunansa dukan al'ummai su gaskata su yi biyayya, 6 t a cikinsu kuma har da ku da kuke kirayayyun Yesu Almasihu.
7 t Daga Bulus zuwa ga dukan ƙaunatattun Allah da kuke a Roma, tsarkaka kirayayyu.
Alheri da salama na Allah Ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.Nufin Bulus Ya Ziyarci Roma
8 t Da farko dai ina gode wa Allahna ta wurin Yesu Almasihu saboda ku duka, domin ana baza labarin bangaskiyarku a ko'ina a duniya. 9 t Domin kuwa Allah, wanda nake bauta wa a ruhuna ta yin bisharar Ɗansa, shi ne mashaidina a kan yadda kullum ba na fasa ambatonku a cikin addu'ata, 10 t ina addu'a, ko ta ƙaƙa, da yardar Allah, a yanzu kam, in sami arzikin zuwa wurinku. 11 t Domin ina ɗokin ganinku, in ni'imta ku da wata baiwa ta ruhu, domin ku ƙarfafa. 12 Wato ni da ku, mu ƙarfafa juna ta bangaskiyarmu, tawa da taku. 13 t Ina so ku sani 'yan'uwa, na sha ɗaura niyyar zuwa wurinku, ko da yake har yanzu ba a yardar mini ba, domin ku ma in sami amfani a gare ku, kamar yadda na samu a cikin al'ummai. 14 t Akwai hakkin Helenawa, da na bare, da na masu ilimi, da na jahilai duka a kaina.
15 t Saboda haka a gwargwadon iyawata, ina da himma ku ma in yi muku bisharar, ku da kuke a Roma.Ikon Bishara
16 t Gama ba na jin kunyar bishara, domin ita ce ikon Allah mai kai kowane mai ba da gaskiya ga samun ceto, Yahudawa da fari, sa'an nan kuma al'ummai.
17 t Gama bishara ɗin ta bayyana wata hanyar samun adalci a gaban Allah, hanyar nan kuwa ta bangaskiya ce, tun daga farko har zuwa ƙarshe, yadda yake a rubuce cewa, “Wanda yake da adalci ta wurin bangaskiya zai rayu.”Laifin 'Yan Adam
18 t Gama ana bayyana fushin Allah daga Sama, a kan dukan rashin bin Allah, da aikin mugunta na mutanen da suke danne gaskiya, ta aikin muguntarsu, 19 t Domin abin da za a iya sani a game da Allah a bayyane yake a gare su, gama Allah ne ya bayyana musu shi. 20 t Gama tun daga halittar duniya al'amuran Allah marasa gănuwa, wato ikonsa madawwami, da allahntakarsa, sun fahimtu sarai, ta hanyar abubuwan da aka halitta kuma ake gane su. Saboda haka mutane sun rasa hanzari. 21 t Domin kuwa ko da yake sun san da Allah, duk da haka ba su ɗaukaka shi a kan shi Allah ne ba, ba su kuma gode masa ba. Sai tunaninsu ya wofince, zuciyarsu marar fahimta kuma ta duhunta. 22 t Suna da'awa cewa, su masu hikima ne, sai suka zama wawaye.
23 t Sun sauya ɗaukakar Allah marar mutuwa da misalin siffar mutum mai mutuwa, da ta tsuntsaye, da ta dabbobi, da kuma ta masu jan ciki.
24 t Saboda haka Allah ya sallama su ga rashin tsarkaka ta mugayen sha'awace-sha'awacensu, har su wulakanta jikinsu a junansu,
25 t saboda sun sauya gaskiyar Allah da ƙarya, har yi wa halitta ibada, sun kuma bauta mata, sun ƙi su yi wa Mahalicci, shi wanda yabo ya tabbata a gare shi har abada. Amin.
26 t Don haka Allah ya sallama su ga mugayen sha'awace-sha'awace masu banƙyama, har matansu suka sauya ɗabi'arsu ta halal, da wadda take ta haram.
27 t Haka kuma maza suka bar ma'amalarsu ta halal da mata, jarabar juna ta ɗebe su, maza da maza suna aikata rashin kunya, suna jawo wa kansu sakamako daidai da bauɗewarsu.
28 t Tun da yake sun ƙi su yarda su san Allah, Allah ya sallama su ga halin banza, su aikata abin kunya. 29 t Su masu aikata rashin adalci ne ƙwarai, da mugunta, da kwaɗayi, da ƙeta. Masu hassada ne, da kisankai, da jayayya, da ha'inci, da kuma nukura gaya matuƙa. Macizan ƙaiƙayi ne, 30 t da masu yanke, da maƙiyan Allah, da masu cin mutunci, da masu girmankai, da masu ruba, da masu haddasa mugunta, da marasa bin iyaye, 31 t da marasa fahimta, da masu ta da alkawari, da marasa ƙauna, da marasa tausayi. 32 t Waɗannan kuwa ko da yake sun san shari'ar Allah cewa masu yin irin waɗannan abubuwa, sun cancanci mutuwa, duk da haka, ba aikata su kaɗai suke yi ba, har ma suna goyon masu yinsu.
Romans 1
1 Paul, a servant of Jesus Christ, called to be an apostle, separated unto the gospel of God,2 which he promised afore through his prophets in the holy scriptures,3 concerning his Son, who was born of the seed of David according to the flesh,4 who was declared to be the Son of God with power, according to the spirit of holiness, by the resurrection from the dead; even Jesus Christ our Lord,5 through whom we received grace and apostleship, unto obedience of faith among all the nations, for his name’s sake;6 among whom are ye also called to be Jesus Christ’s:7 To all that are in Rome, beloved of God, called to be saints: Grace to you and peace from God our Father and the Lord Jesus Christ.8 First, I thank my God through Jesus Christ for you all, that your faith is proclaimed throughout the whole world.9 For God is my witness, whom I serve in my spirit in the gospel of his Son, how unceasingly I make mention of you, always in my prayers10 making request, if by any means now at length I may be prospered by the will of God to come unto you.11 For I long to see you, that I may impart unto you some spiritual gift, to the end ye may be established;12 that is, that I with you may be comforted in you, each of us by the other’s faith, both yours and mine.13 And I would not have you ignorant, brethren, that oftentimes I purposed to come unto you (and was hindered hitherto), that I might have some fruit in you also, even as in the rest of the Gentiles.14 I am debtor both to Greeks and to Barbarians, both to the wise and to the foolish.15 So, as much as in me is, I am ready to preach the gospel to you also that are in Rome.16 For I am not ashamed of the gospel: for it is the power of God unto salvation to every one that believeth; to the Jew first, and also to the Greek.17 For therein is revealed a righteousness of God from faith unto faith: as it is written, But the righteous shall live by faith.18 For the wrath of God is revealed from heaven against all ungodliness and unrighteousness of men, who hinder the truth in unrighteousness;19 because that which is known of God is manifest in them; for God manifested it unto them.20 For the invisible things of him since the creation of the world are clearly seen, being perceived through the things that are made, even his everlasting power and divinity; that they may be without excuse:21 because that, knowing God, they glorified him not as God, neither gave thanks; but became vain in their reasonings, and their senseless heart was darkened.22 Professing themselves to be wise, they became fools,23 and changed the glory of the incorruptible God for the likeness of an image of corruptible man, and of birds, and four-footed beasts, and creeping things.24 Wherefore God gave them up in the lusts of their hearts unto uncleanness, that their bodies should be dishonored among themselves:25 for that they exchanged the truth of God for a lie, and worshipped and served the creature rather than the Creator, who is blessed for ever. Amen.26 For this cause God gave them up unto vile passions: for their women changed the natural use into that which is against nature:27 and likewise also the men, leaving the natural use of the woman, burned in their lust one toward another, men with men working unseemliness, and receiving in themselves that recompense of their error which was due.28 And even as they refused to have God in their knowledge, God gave them up unto a reprobate mind, to do those things which are not fitting;29 being filled with all unrighteousness, wickedness, covetousness, maliciousness; full of envy, murder, strife, deceit, malignity; whisperers,30 backbiters, hateful to God, insolent, haughty, boastful, inventors of evil things, disobedient to parents,31 without understanding, covenant-breakers, without natural affection, unmerciful:32 who, knowing the ordinance of God, that they that practise such things are worthy of death, not only do the same, but also consent with them that practise them.