previous next

ROM 10

1 Ya 'yan'uwa, muradin zuciyata da kuma roƙona ga Allah saboda su, shi ne su sami ceto. 2 t Na dai shaida su a kan suna da himmar bauta wa Allah, amma ba da cikakken sani ba. 3 t Don saboda rashin fahimtar hanyar samun adalci, wadda Allah ya tanadar, da kuma neman kafa tāsu hanya, sai suka ƙi bin ita wannan hanya ta samun adalci wadda Allah ya tanadar.

4 t Domin Almasihu shi ne cikamakin Shari'a, domin kowane mai ba da gaskiya yă sami adalcin Allah.
5  t Gama Musa ya rubuta zancen adalcin da yake samuwa ta wurin bin Shari'a, cewa mai iya aikata ta zai rayu ta wurinta. 6 t Amma, a game da samun adalcin Allah wanda yake ta wurin bangaskiya ya ce, Kada ka ce a ranka, “Wa zai hau zuwa sama?” Wato, yă sauko da Almasihu. 7 Ko kuwa, “Wa zai gangara can ƙasa?” Wato yă ta da Almasihu daga matattu. 8 t Amma me Nassi ya ce? “Maganar, ai, tana kusa da kai, tana ma a bakinka, da kuma a cikin zuciyarka.” Ita ce maganar bangaskiya da muke wa'azi. 9 t Wato, in kai da bakinka ka bayyana yarda, cewa Yesu Ubangiji ne, ka kuma gaskata a zuciyarka Allah ya tashe shi daga matattu, za ka sami ceto. 10 Domin da zuci mutum yake gaskatawa yă sami adalcin Allah, da baki yake shaidawa yă sami ceto. 11 t Gama Nassi ya ce, “Duk mai gaskatawa da shi ba zai kunyata ba.” 12 t Ai, ba wani bambanci a tsakanin Bayahude da Ba'al'umme. Ubangijin nan ɗaya shi ne Ubangijin kowa, mayalwacin baiwa ne kuma ga dukkan masu addu'a a gare shi.

13 t “Duk wanda kuwa ya yi addu'a da sunan Ubangiji zai sami ceto.”
14 Amma ta ƙaƙa za su yi addu'a ga wanda ba su gaskata da shi ba? Ta ƙaƙa kuma za su gaskata da wanda ba su taɓa ji ba? Ta ƙaƙa kuma za su ji, in ba mai wa'azi? 15 t Ta ƙaƙa kuma za su yi wa'azi, in ba aikarsu aka yi ba? Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yaya zai kasance a isowar masu kawo bishara!” 16 t Amma ba duka ne suka yi na'am da bisharar ba. Ishaya ma ya ce, “Ya Ubangiji, wa ya gaskata jawabinmu?”

17 t Ashe, bangaskiya ta wurin jawabin da ake ji take samuwa, jawabin da ake ji kuma ta Maganar Almasihu yake.

18  t Amma ina tambaya. Ba su ji jawabin ba ne? Hakika sun ji.
“Muryarsu ta gama duniya duka,
Maganarsu kuma ta kai har bangon duniya.”

19  t Har wa yau, ina tambaya. Shin, Isra'ila kam, ba su fahimta ba ne? Da farko dai Musa ya ce,
“Zan sa ku kishin waɗanda ba al'umma ba ne,
Zan kuma sa ku fushi da wata al'ummar marar fahimta.”

20  t Ishayan kuma ya fito gabagaɗi ƙwarai ya ce,
“Waɗanda ba su neme ni ba, su suka same ni.
Na bayyana kuma ga waɗanda ba su taɓa neman sanina ba.”
21  t Amma a game da isra'ila, sai ya ce, “Yini zubur ina miƙa hannuwana ga jama'a marasa biyayya, masu tsayayya.”

Romans 10

1 Brethren, my heart’s desire and my supplication to God is for them, that they may be saved.2 For I bear them witness that they have a zeal for God, but not according to knowledge.3 For being ignorant of God’s righteousness, and seeking to establish their own, they did not subject themselves to the righteousness of God.4 For Christ is the end of the law unto righteousness to every one that believeth.5 For Moses writeth that the man that doeth the righteousness which is of the law shall live thereby.6 But the righteousness which is of faith saith thus, Say not in thy heart, Who shall ascend into heaven? (that is, to bring Christ down:)7 or, Who shall descend into the abyss? (That is, to bring Christ up from the dead.)8 But what saith it? The word is nigh thee, in thy mouth, and in thy heart: that is, the word of faith, which we preach:9 because if thou shalt confess with thy mouth Jesus as Lord, and shalt believe in thy heart that God raised him from the dead, thou shalt be saved:10 for with the heart man believeth unto righteousness; and with the mouth confession is made unto salvation.11 For the scripture saith, Whosoever believeth on him shall not be put to shame.12 For there is no distinction between Jew and Greek: for the same Lord is Lord of all, and is rich unto all that call upon him:13 for, Whosoever shall call upon the name of the Lord shall be saved.14 How then shall they call on him in whom they have not believed? and how shall they believe in him whom they have not heard? and how shall they hear without a preacher?15 and how shall they preach, except they be sent? even as it is written, How beautiful are the feet of them that bring glad tidings of good things!16 But they did not all hearken to the glad tidings. For Isaiah saith, Lord, who hath believed our report?17 So belief cometh of hearing, and hearing by the word of Christ.18 But I say, Did they not hear? Yea, verily, Their sound went out into all the earth, And their words unto the ends of the world.

19 But I say, Did Israel not know? First Moses saith, I will provoke you to jealousy with that which is no nation, With a nation void of understanding will I anger you.

20 And Isaiah is very bold, and saith, I was found of them that sought me not; I became manifest unto them that asked not of me.

21 But as to Israel he saith, All the day long did I spread out my hands unto a disobedient and gainsaying people.