ROM 12
Hadaya Mai Rai
1 t Don haka ina roƙonku 'yan'uwa, saboda yawan jinƙai na Allah, ku miƙa jikinku hadaya rayayyiya, tsattsarka, abar karɓa ga Allah. Domin wannan ita ce ibadarku ta ainihi.
2 t Kada ku biye wa zamanin nan, amma ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so, wato nufinsa kyakkyawa, abin karɓa, cikakke kuma.
3 t Albarkacin alherin da aka yi mini ina yi wa kowannenku gargaɗi kada ya ɗauki kansa fiye da yadda ya kamata, sai dai ya san kansa, gwargwadon bangaskiyar da Allah ya ba shi. 4 t Wato kamar yadda gaɓoɓi da yawa suke harhaɗe a jiki ɗaya, gaɓoɓin nan kuwa ba aiki iri ɗaya suke yi ba, 5 t haka mu ma, ko da yake muna da yawa, jiki ɗaya muke haɗe da Almasihu, kowannenmu kuma gaɓar ɗan'uwansa ne. 6 t Da yake muna da baiwa iri iri, gwargwadon alherin da aka yi mana, to, sai mu yi amfani da su. In ta annabci ce, sai mu yi amfani da ita gwargwadon bangaskiyarmu, 7 t in ta hidima ce, wajen hidimarmu, mai koyar da Maganar Allah kuwa, wajen koyarwarsa,
8 t mai ƙarfafa zuciya kuwa, wajen ƙarfafawarsa, mai yin gudunmawa kuwa, yă bayar hannu sake, shugaba yă yi shugabancinsa da himma, mai yin aikin tausayi, yă yi shi da fara'a.Gargaɗi a kan Zaman Kirista
9 t Ƙauna ta kasance sahihiya. Ku yi ƙyamar abin da yake mugu, ku lazamci abin da yake nagari. 10 t A game da ƙaunar 'yan'uwa kuwa, ku ƙaunaci juna gaya. A wajen ba da girma, kowa yă riga ba ɗan'uwansa. 11 t Kada ku sassauta a wajen himma, ku himmantu a ruhu, kuna bauta wa Ubangiji. 12 t Sa zuciyar nan taku ta sa ku farin ciki, ku jure wa wahala, ku nace wa yin addu'a.
13 t Ku agaji tsarkaka, ku himmantu ga yi wa baƙi alheri.
14 t Ku sa wa masu tsananta muku albarka. Ku sa musu albarka, kada ku la'ance su. 15 t Ku taya masu farin ciki farin ciki, masu kuka kuwa ku taya su kuka. 16 t Ku yi zaman lafiya da juna. Kada ku nuna alfarma, sai dai ku miƙa kanku ga aikata ayyukan tawali'u. Kada ku aza kanku masu hikima ne. 17 t Kada ku rama muguntar kowa da mugunta. Ku yi ta lura al'amuranku su zama daidai a gaban kowa. 18 t In mai yiwuwa ne, a gare ku, ku yi zaman lafiya da kowa. 19 t Ya ku ƙaunatattuna, kada ku ku yi ramuwa, sai dai ku bar wa fushin Allah. Domin a rubuce yake cewa, “Ramuwa tawa ce, ni zan saka, in ji Ubangiji.” 20 t Har ma “in maƙiyinka yana jin yunwa, sai ka ci da shi. In yana jin ƙishirwa, ka shayar da shi. Don ta haka ne za ka tula garwashin wuta a kansa.” 21 Kada mugunta ta rinjaye ku, amma ku rinjayi mugunta da nagarta.
Romans 12
1 I beseech you therefore, brethren, by the mercies of God, to present your bodies a living sacrifice, holy, acceptable to God, which is your spiritual service.2 And be not fashioned according to this world: but be ye transformed by the renewing of your mind, and ye may prove what is the good and acceptable and perfect will of God.3 For I say, through the grace that was given me, to every man that is among you, not to think of himself more highly than he ought to think; but to think as to think soberly, according as God hath dealt to each man a measure of faith.4 For even as we have many members in one body, and all the members have not the same office:5 so we, who are many, are one body in Christ, and severally members one of another.6 And having gifts differing according to the grace that was given to us, whether prophecy, let us prophesy according to the proportion of our faith;7 or ministry, let us give ourselves to our ministry; or he that teacheth, to his teaching;8 or he that exhorteth, to his exhorting: he that giveth, let him do it with liberality; he that ruleth, with diligence; he that showeth mercy, with cheerfulness.9 Let love be without hypocrisy. Abhor that which is evil; cleave to that which is good.10 In love of the brethren be tenderly affectioned one to another; in honor preferring one another;11 in diligence not slothful; fervent in spirit; serving the Lord;12 rejoicing in hope; patient in tribulation; continuing stedfastly in prayer;13 communicating to the necessities of the saints; given to hospitality.14 Bless them that persecute you; bless, and curse not.15 Rejoice with them that rejoice; weep with them that weep.16 Be of the same mind one toward another. Set not your mind on high things, but condescend to things that are lowly. Be not wise in your own conceits.17 Render to no man evil for evil. Take thought for things honorable in the sight of all men.18 If it be possible, as much as in you lieth, be at peace with all men.19 Avenge not yourselves, beloved, but give place unto the wrath of God: for it is written, Vengeance belongeth unto me; I will recompense, saith the Lord.20 But if thine enemy hunger, feed him; if he thirst, give him to drink: for in so doing thou shalt heap coals of fire upon his head.21 Be not overcome of evil, but overcome evil with good.