previous next

ROM 13

1  t Bari kowa yă yi biyayya ga mahukunta. Gama ba wani iko sai da yardar Allah. Mahukuntan da suke nan kuwa naɗin Allah ne. 2 Saboda haka duk wanda ya yi wa mahukunta tsayayya, ya yi wa umarnin Allah ke nan, masu yin tsayayyar nan kuwa za a yi musu hukunci. 3 t Don kuwa mahukunta ba abin tsoro ba ne ga masu aiki nagari, sai dai ga masu mugun aiki. Kana so kada ka ji tsoron mahukunci? To, sai ka yi nagarta, sai kuwa ya yaba maka. 4 t Domin shi bawan Allah ne, don kyautata zamanka. Amma in kai mai mugun aiki ne, to, ka ji tsoro, don ba a banza yake riƙe da takobi ba. Ai, shi bawa ne na Allah, mai sāka wa mugu da fushi. 5 Saboda haka wajibi ne ka yi biyayya, ba domin gudun fushi kaɗai ba, amma domin lamiri kuma. 6 Shi ne ma ya sa kuke biyan haraji, don su mahukunta ma'aikata ne na Allah, suna kuma yin wannan aiki a koyaushe. 7 t Ku ba kowa hakkinsa, masu haraji, harajinsu, masu kuɗin fito, kuɗinsu na fito, waɗanda suka cancanci ladabi, ladabi, waɗanda suka cancanci girmamawa, girmamawa. 8 t Kada hakkin kowa ya zauna a kanku, sai dai na ƙaunar juna, don mai ƙaunar maƙwabcinsa ya cika Shari'a ke nan. 9 t Umarnan nan cewa, “kada ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kada ka yi ƙyashi,” da dai duk sauran umarnai an ƙunshe su ne a wannan kalma cewa, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”

10 t Ƙauna ba ta cutar maƙwabci saboda haka ƙauna cika Shari'a ce.
11  t Ga shi kuma, kun dai san irin zamanin da muke a ciki, ai, lokaci ya riga ya yi da za ku farka daga barci. Gama yanzu mun fi kusa da ceton nan namu a kan sa'ad da muka fara ba da gaskiya. 12 Dare fa ya ƙure, gari ya kusa wayewa. Sai mu watsar da ayyukan duhu, mu yi ɗamara da kayan ɗamara na haske. 13 t Mu tafiyar da al'amuranmu yadda ya dace a yi da rana, ba a cikin shashanci da buguwa, ko fasikanci da fajirci, ko jayayya da kishi ba. 14 t Amma ku ɗauki halin Ubangiji Yesu Almasihu, kada kuwa ku tanadi halin mutuntaka, don biye wa muguwar sha'awarsa.

Romans 13

1 Let every soul be in subjection to the higher powers: for there is no power but of God; and the powers that be are ordained of God.2 Therefore he that resisteth the power, withstandeth the ordinance of God: and they that withstand shall receive to themselves judgment.3 For rulers are not a terror to the good work, but to the evil. And wouldest thou have no fear of the power? do that which is good, and thou shalt have praise from the same:4 for he is a minister of God to thee for good. But if thou do that which is evil, be afraid; for he beareth not the sword in vain: for he is a minister of God, an avenger for wrath to him that doeth evil.5 Wherefore ye must needs be in subjection, not only because of the wrath, but also for conscience’ sake.6 For this cause ye pay tribute also; for they are ministers of God’s service, attending continually upon this very thing.7 Render to all their dues: tribute to whom tribute is due; custom to whom custom; fear to whom fear; honor to whom honor.8 Owe no man anything, save to love one another: for he that loveth his neighbor hath fulfilled the law.9 For this, Thou shalt not commit adultery, Thou shalt not kill, Thou shalt not steal, Thou shalt not covet, and if there be any other commandment, it is summed up in this word, namely, Thou shalt love thy neighbor as thyself.10 Love worketh no ill to his neighbor: love therefore is the fulfilment of the law.11 And this, knowing the season, that already it is time for you to awake out of sleep: for now is salvation nearer to us than when we first believed.12 The night is far spent, and the day is at hand: let us therefore cast off the works of darkness, and let us put on the armor of light.13 Let us walk becomingly, as in the day; not in revelling and drunkenness, not in chambering and wantonness, not in strife and jealousy.14 But put ye on the Lord Jesus Christ, and make not provision for the flesh, to fulfil the lusts thereof.