ROM 15
Faranta wa Ɗan'uwanka Rai, ba kanka Ba
1 t To, mu da muke ƙarfafa, ya kamata mu ɗauki nauyin raunana, kada mu yi sonkai. 2 t Kowannenmu yă faranta wa maƙwabcinsa rai, don kyautata zamansa da kuma inganta shi. 3 t Gama ko Almasihu ma bai yi sonkai ba, amma kamar yadda yake a rubuce cewa, “Zagin da waɗansu suka yi maka duk yā komo kaina.” 4 t Ai, duk abin da aka rubuta tun dā, an rubuta shi ne domin a koya mana, domin mu ɗore a cikin sa zuciyar nan tamu ta wurin haƙuri da ta'aziyyar da Littattafai suke yi mana. 5 t Allah mai ba da haƙuri da ta'aziyya, yă ba ku zaman lafiya da juna bisa halin Almasihu Yesu,
6 t domin ku ɗaukaka Allah, Ubangijinmu Yesu Almasihu, da kuma Ubansa, nufinku ɗaya, bakinku ɗaya.Bishara ga Al'ummai
7 t Saboda haka ku karɓi juna da hannu biyu biyu, kamar yadda Almasihu ya karɓe ku hannu biyu biyu, domin a ɗaukaka Allah. 8 t Ina dai gaya muku, Almasihu ya zama bara ga Isra'ila, domin nuna gaskiyar Allah, domin kuma tabbatar da alkawaran nan, da Allah ya yi wa kakannin kakanninmu,
9 t al'ummai kuma su ɗaukaka Allah saboda jinƙansa. Yadda yake a rubuce,
“Domin haka zan yabe ka a cikin al'ummai,
In kuma yi waƙar yabon sunanka.”
10 t Har wa yau kuma an ce,
“Ya ku al'ummai, ku yi ta farin ciki tare da jama'arsa.”
11 t Da kuma,
“Ku yabi Ubangiji, ya ku al'ummai duka,
Dukkan kabilai kuma su yabe shi.”
12 t Ishaya kuma ya ce,
“Tsatson Yesse zai bayyana,
Wanda zai tashi yă mallaki al'ummai,
A gare shi ne al'ummai za su sa zuciya.”
13 t Allah mai kawo sa zuciya, yă cika ku da matuƙar farin ciki da salama saboda bangaskiyarku, domin ku yi matuƙar sa zuciya ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.
14 t Ya 'yan'uwana, ni ma da kaina na amince da ku, cewa ku da kanku masu nagarta ne ƙwarai da gaske, masu cikakken sani, kun kuma isa ku gargaɗi juna. 15 t Duk da haka, a kan waɗansu batatuwan da na rubuto muku, na ƙara ƙarfafawa ƙwarai, domin tuni, saboda alherin da Allah ya yi mini 16 t da ya sa ni bawan Almasihu Yesu ga al'ummai, ina hidimar bisharar Allah, domin al'ummai su zama hadaya mai karɓuwa a gare shi, tsattsarka ta wurin Ruhu Mai Tsarki. 17 t Ashe kuwa, ina da dalilin yin alfarma da Almasihu Yesu a game da al'amarin Allah. 18 t Ba zan kuskura in faɗi kome ba, sai abin da Almasihu ya aikata ta wurina, a wajen sa al'ummai biyayya ta wurin maganata da aikina, 19 t ta wurin ikon mu'ujizai, da abubuwan al'ajabai, da kuma ta wurin ikon Ruhun, har dai daga Urushalima da kewayenta, har zuwa Ilirikun, na yi bisharar Almasihu a ko'ina. 20 t Har ya zama mini abin buri in sanar da bishara, a inda ba a taɓa sanar da sunan Almasihu ba, don kada in ɗora ginina a kan harsashin wani,
21 t sai dai kamar yadda yake a rubuce,
“Waɗanda ba a taɓa faɗa wa labarinsa ba, za su gane,
Waɗanda ba su taɓa jin labarinsa ba ma, za su fahimta.”Bulus Ya Shirya yă Ziyarci Roma
22 t Shi ya sa sau da yawa ban sami sukunin zuwa wurinku ba. 23 t A yanzu kuwa tun da yake ba sauran wani wuri da ya rage mini a lardin nan, shekaru da yawa kuma ina ɗokin zuwa wurinku, 24 t ina sa zuciya in gan ku, in zan wuce zuwa ƙasar Asbaniya, har ma ku raka ni zuwa can, bayan da na ɗan ɗebe kewa da ganinku. 25 t Amma a yanzu kam, za ni Urushalima, don in kai wa tsarkaka gudunmawa. 26 t Mutanen Makidoniya da na Akaya, sun ji daɗin yin gudunmawar daidai gwargwado ga matalauta, a cikin tsarkakan da suke a Urushalima. 27 t Sun kuwa ji daɗin yin haka, domin hakika kamar bashi ne a kansu. Domin tun da yake al'ummai sun yi tarayya da su a kan ni'imarsu ta ruhu, ashe kuwa, ya kamata su ma su taimake su da ni'imarsu ta duniya. 28 In kuwa na gama wannan, na kuma danƙa musu wannan taimako lafiya, sai in bi ta kanku zuwa ƙasar Asbaniya.
29 t Na kuma sani, in na zo wurinku, zan zo ne a cikin falalar albarkar Almasihu
30 t Amma ina roƙonku 'yan'uwa, saboda Ubangijinmu Yesu Almasihu, da kuma ƙaunar nan da Ruhu yake bayarwa, ku taya ni yin addu'a da naciya ga Allah saboda kaina, 31 t domin in tsira daga maƙiyan bangaskiya a Yahudiya, don kuma gudunmawar da nake kaiwa Urushalima, ta zama abar karɓa ga tsarkaka, 32 t har in Allah ya yarda in iso wurinku da farin ciki, mu wartsake tare. 33 t Allah mai ba da salama ya kasance tare da ku duka. Amin.
Romans 15
1 Now we that are strong ought to bear the infirmities of the weak, and not to please ourselves.2 Let each one of us please his neighbor for that which is good, unto edifying.3 For Christ also pleased not himself; but, as it is written, The reproaches of them that reproached thee fell upon me.4 For whatsoever things were written aforetime were written for our learning, that through patience and through comfort of the scriptures we might have hope.5 Now the God of patience and of comfort grant you to be of the same mind one with another according to Christ Jesus:6 that with one accord ye may with one mouth glorify the God and Father of our Lord Jesus Christ.7 Wherefore receive ye one another, even as Christ also received you, to the glory of God.8 For I say that Christ hath been made a minister of the circumcision for the truth of God, that he might confirm the promises given unto the fathers,9 and that the Gentiles might glorify God for his mercy; as it is written, Therefore will I give praise unto thee among the Gentiles, And sing unto thy name.
10 And again he saith, Rejoice, ye Gentiles, with his people.
11 And again, Praise the Lord, all ye Gentiles; And let all the peoples praise him.
12 And again, Isaiah saith, There shall be the root of Jesse, And he that ariseth to rule over the Gentiles; On him shall the Gentiles hope.
13 Now the God of hope fill you with all joy and peace in believing, that ye may abound in hope, in the power of the Holy Spirit.14 And I myself also am persuaded of you, my brethren, that ye yourselves are full of goodness, filled with all knowledge, able also to admonish one another.15 But I write the more boldly unto you in some measure, as putting you again in remembrance, because of the grace that was given me of God,16 that I should be a minister of Christ Jesus unto the Gentiles, ministering the gospel of God, that the offering up of the Gentiles might be made acceptable, being sanctified by the Holy Spirit.17 I have therefore my glorifying in Christ Jesus in things pertaining to God.18 For I will not dare to speak of any things save those which Christ wrought through me, for the obedience of the Gentiles, by word and deed,19 in the power of signs and wonders, in the power of the Holy Spirit; so that from Jerusalem, and round about even unto Illyricum, I have fully preached the gospel of Christ;20 yea, making it my aim so to preach the gospel, not where Christ was already named, that I might not build upon another man’s foundation;21 but, as it is written, They shall see, to whom no tidings of him came, And they who have not heard shall understand.
22 Wherefore also I was hindered these many times from coming to you:23 but now, having no more any place in these regions, and having these many years a longing to come unto you,24 whensoever I go unto Spain (for I hope to see you in my journey, and to be brought on my way thitherward by you, if first in some measure I shall have been satisfied with your company)--25 but now, I say, I go unto Jerusalem, ministering unto the saints.26 For it hath been the good pleasure of Macedonia and Achaia to make a certain contribution for the poor among the saints that are at Jerusalem.27 Yea, it hath been their good pleasure; and their debtors they are. For if the Gentiles have been made partakers of their spiritual things, they owe it to them also to minister unto them in carnal things.28 When therefore I have accomplished this, and have sealed to them this fruit, I will go on by you unto Spain.29 And I know that, when I come unto you, I shall come in the fulness of the blessing of Christ.30 Now I beseech you, brethren, by our Lord Jesus Christ, and by the love of the Spirit, that ye strive together with me in your prayers to God for me;31 that I may be delivered from them that are disobedient in Judaea, and that my ministration which I have for Jerusalem may be acceptable to the saints;32 that I may come unto you in joy through the will of God, and together with you find rest.33 Now the God of peace be with you all. Amen.