ROM 7
Ƙiyasi da Aure
1 t Ya 'yan'uwa, ko ba ku sani ba, shari'a tana da iko da mutum, muddin yana raye ne kawai? Da waɗanda suka san shari'a fa nake. 2 t Misali, mace mai aure, shari'a ta ɗaure ta ga mijinta muddin yana da rai. Amma in mijinta ya mutu, ta kuɓuta daga igiyar auren ke nan.
3 Don haka, muddin mijinta yana da rai, in ta auri wani, sai a kira ta mazinaciya. Amma in mijinta ya mutu, ta kuɓuta daga igiyar wannan aure, ko da ta auri wani kuwa, ita ba mazinaciya ba ce.
4 t Haka kuma 'yan'uwana, kun zama matattu ga Shari'a, ta wurin jikin Almasihu, domin ku zama mallakar wani, wato, wanda aka tashe shi daga matattu, domin mu ba da amfani ga Allah. 5 t Ai, dā sa'ad da muke zaman halin mutuntaka, muguwar sha'awa wadda faɗakarwar Shari'a take sa a yi, ita take aiki a gaɓoɓinmu, tă wurin haddasa mutuwa.
6 t Amma a yanzu mun 'yantu daga Shari'a, mun mutu daga abin da dā ya ɗaure mu ke nan, har muna iya bauta wa Allah da sabon rai da Ruhu, ba da tsofaffin rubutattun ka'idodi ba.Damuwa wadda Zunubin da Yake a Cikinmu Take Haddasawa
7 t To, me kuma za mu ce? Shari'a zunubi ce? A'a, ko kusa! Amma kuwa duk da haka, da ba domin Shari'a ba, da ban san zunubi ba. Da ba domin Shari'a ta ce, “Kada ka yi ƙyashi” ba, da ban san ƙyashi ba. 8 t Amma zunubi, da ya sami ƙofa ta hanyar umarni, sai ya haddasa ƙyashi iri iri a zuciyata. Gama da ba domin shari'a ba, da zunubi ba shi da wani tasiri. 9 Dā kam, sa'ad da ban san shari'a ba, ni rayayye ne, amma da na san umarnin, sai zunubi ya rayu, ni kuma sai na mutu. 10 t Umarnin nan kuwa, wanda manufarsa a gare ni rai ne, sai ya jawo mini mutuwa. 11 t Don kuwa zunubi ya sami ƙofa ta hanyar umarni, sai ya yaudare ni, ta wurinsa kuwa ya kashe ni.
12 t Domin haka Shari'a da kanta mai tsarki ce, umarnin kuma mai tsarki ne, daidai ne, nagari ne.
13 Wato, abar nan da take tagari ta jawo mini mutuwa ke nan? A'a, ko kusa! Zunubi ne ya jawo, domin ya bayyana kansa shi zunubi ne, gama ta wurin abar nan tagari ya jawo mini mutuwa, ta dalilin umarnin nan kuma, zunubi ya bayyana matuƙar muninsa. 14 t Mun dai san Shari'a aba ce ta ruhu, ni kuwa mai halin mutuntaka ne, bautar zunubi kawai nake yi. 15 t Ban ma fahimci abin da nake yi ba. Don ba abin da nake niyya yi, ba shi nake aikatawa ba, abin da nake ƙi, shi nake yi. 16 t To, idan abin da ba na niyya, shi nake yi, na yarda ke nan Shari'a aba ce mai kyau. 17 t Ashe kuwa, ba ni nake yinsa ba ke nan, zunubin da ya zaune mini ne. 18 t Don na sani ba wani abin kirki da ya zaune mini, wato a jikina. Niyyar yin abin da yake daidai kam, ina da ita, sai dai ikon zartarwar ne babu. 19 t Nagarin abin da nake niyya yi kuwa, ba shi nake yi ba, sai dai mugun abin da ba na niyya, shi nake aikatawa.
20 t To, idan abin da ba na niyya shi nake yi, ashe kuwa, ba ni nake yinsa ba ke nan, zunubin da ya zaune mini ne.
21 t Sai na ga, ashe, ya zama mini ka'ida, in na so yin abin da yake daidai, sai in ga mugunta tare da ni. 22 t Ni kam, a birnin zuciyata, na amince da shari'ar Allah. 23 t Amma ina ganin wata ka'ida dabam a gaɓoɓina, wadda take yaƙi da ka'idar da hankalina ya ɗauka, har tana mai da ni bawan ƙa'idar nan ta zunubi wadda take zaune a gaɓoɓina. 24 t Kaitona! Wa zai cece ni daga jikin nan, wanda yake kai ni ga mutuwa? 25 Godiya tā tabbata ga Allah, akwai, ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu! Ashe kuwa, ni a kaina, da hankalina, hakika Shari'ar Allah nake bauta wa, amma da jikina ka'idar zunubi nake bauta wa.
Romans 7
1 Or are ye ignorant, brethren (for I speak to men who know the law), that the law hath dominion over a man for so long time as he liveth?2 For the woman that hath a husband is bound by law to the husband while he liveth; but if the husband die, she is discharged from the law of the husband.3 So then if, while the husband liveth, she be joined to another man, she shall be called an adulteress: but if the husband die, she is free from the law, so that she is no adulteress, though she be joined to another man.4 Wherefore, my brethren, ye also were made dead to the law through the body of Christ; that ye should be joined to another, even to him who was raised from the dead, that we might bring forth fruit unto God.5 For when we were in the flesh, the sinful passions, which were through the law, wrought in our members to bring forth fruit unto death.6 But now we have been discharged from the law, having died to that wherein we were held; so that we serve in newness of the spirit, and not in oldness of the letter.7 What shall we say then? Is the law sin? God forbid. Howbeit, I had not known sin, except through the law: for I had not known coveting, except the law had said, Thou shalt not covet:8 but sin, finding occasion, wrought in me through the commandment all manner of coveting: for apart from the law sin is dead.9 And I was alive apart from the law once: but when the commandment came, sin revived, and I died;10 and the commandment, which was unto life, this I found to be unto death:11 for sin, finding occasion, through the commandment beguiled me, and through it slew me.12 So that the law is holy, and the commandment holy, and righteous, and good.13 Did then that which is good become death unto me? God forbid. But sin, that it might be shown to be sin, by working death to me through that which is good; --that through the commandment sin might become exceeding sinful.14 For we know that the law is spiritual: but I am carnal, sold under sin.15 For that which I do I know not: for not what I would, that do I practise; but what I hate, that I do.16 But if what I would not, that I do, I consent unto the law that it is good.17 So now it is no more I that do it, but sin which dwelleth in me.18 For I know that in me, that is, in my flesh, dwelleth no good thing: for to will is present with me, but to do that which is good is not.19 For the good which I would I do not: but the evil which I would not, that I practise.20 But if what I would not, that I do, it is no more I that do it, but sin which dwelleth in me.21 I find then the law, that, to me who would do good, evil is present.22 For I delight in the law of God after the inward man:23 but I see a different law in my members, warring against the law of my mind, and bringing me into captivity under the law of sin which is in my members.24 Wretched man that I am! who shall deliver me out of the body of this death?25 I thank God through Jesus Christ our Lord. So then I of myself with the mind, indeed, serve the law of God; but with the flesh the law of sin.