ROM 8
Rayuwa a Cikin Ruhu
1 t Saboda haka a yanzu, ba sauran kayarwa ga waɗanda suke na Almasihu Yesu. 2 t Ka'idar nan ta Ruhu mai ba da rai da yake ga Almasihu Yesu ta 'yanta ni daga ka'idar zunubi da ta mutuwa. 3 t Abin da ba shi yiwuwa Shari'a ta yi domin ta kasa saboda halin ɗan adam, Allah ya yi shi, wato ya ka da zunubi a cikin jiki, da ya aiko da Ɗansa da kamannin jikin nan namu mai zunubi, domin kawar da zunubi. 4 t Wannan kuwa domin a cika hakkokin Shari'a ne a gare mu, mu da ba zaman halin mutuntaka muke yi ba, sai dai na Ruhu. 5 t Masu zaman halin mutuntaka, ai, ƙwallafa ransu ga al'amuran halin mutuntaka suke yi, masu zaman Ruhu kuwa ga al'amuran Ruhu. 6 t Ƙwallafa rai ga al'amuran halin mutuntaka ƙarshensa mutuwa ne, ƙwallafa rai ga ala'muran Ruhu kuwa rai ne da salama. 7 t Don ƙwallafa rai ga al'amuran halin mutuntaka gāba ne da Allah, gama ba ya bin Shari'ar Allah, ba kuwa zai iya ba.
8 Masu zaman halin mutuntaka, ba dama su faranta wa Allah rai.
9 t Amma ku kam, ba masu zaman halin mutuntaka ba ne, masu zaman Ruhu ne, in dai har Ruhun Allah yana zaune a zuciyarku. Duk wanda ba shi da Ruhun Almasihu kuwa, ba na Almasihu ba ne. 10 t In kuwa Almasihu yana a zuciyarku, ba ruwan jikinku da zunubi ke nan, Ruhu kuwa rai ne a gare ku saboda kun sami adalcin Allah.
11 t In kuwa Ruhun wannan da ya ta da Yesu daga matattu yana zaune a zuciyarku, to, shi da ya ta da Almasihu Yesu daga matattu zai kuma raya jikin nan naku mai mutuwa, ta wurin Ruhunsa da yake a zaune a zuciyarku.
12 Domin haka, 'yan'uwa, kun ga halin mutuntaka ba shi da wani hakki a kanmu har da za mu yi zamansa. 13 t In kuna zaman halin mutuntaka, za ku mutu ke nan, amma in da ikon Ruhu kuka kashe ayyukan nan na halin mutuntaka, sai ku rayu. 14 t Duk waɗanda Ruhun Allah yake bishe su, su ne 'ya'yan Allah. 15 t Ai, ruhun da kuka samu ba na bauta ba ne, har da za ku koma zaman tsoro. A'a, na zaman 'ya'ya ne, har muna kira, “Ya Abba! Uba!” 16 t Ruhu da Kansa ma, tare da namu ruhu suna yin shaida, cewa mu 'ya'yan Allah ne.
17 t In kuwa 'ya'ya muke, ashe, magāda ne kuma, magādan Allah, abokan gādo kuma da Almasihu, in dai har muna shan wuya tare da shi, a kuwa ɗaukaka mu tare da shi.
18 t Ai, a ganina, wuyar da muke sha a wannan zamani, ba ta isa a kwatanta ta da ɗaukakar da za a bayyana mana ba. 19 Ga shi, duk halitta tana marmari, tana ɗokin ganin bayyanar 'ya'yan Allah. 20 t An sarayar da halitta ta zama banza, ba da nufinta ba, amma da nufin wanda ya sarayar da ita. Duk da haka, akwai sa zuciya, 21 t gama za a 'yantar da halitta da kanta ma, daga bautar ruɓewa, domin ta sami 'yancin nan, na ɗaukaka na 'ya'yan Allah. 22 t Mun dai san dukan halitta tana nishi, na shan azaba kuma irin ta mai naƙuda, har ya zuwa yanzu. 23 t Banda haka ma, har mu kanmu da muka riga muka sami Ruhu Mai Tsarki, wanda yake shi ne nunan fari, a cikin abubuwan da za mu samu, muna nishi a ranmu, muna ɗokin cikar zamanmu na 'ya'yan Allah, wato, fansar jikin nan namu ke nan. 24 t Sa'ad da aka cece mu ne muka yi wannan sa zuciya. Amma kuwa, ai, sa zuciya ga abin da aka samu, ba sa zuciya ba ce. Wa yake sa zuciya ga abin da ya samu?
25 In kuwa muna sa zuciya ga abin da ba mu samu ba, da jimiri mukan yi sauraronsa.
26 t Haka kuma Ruhu yake yi mana taimako a kan gajiyawarmu, domin ba mu ma san abin da ya kamata mu roƙa ba, amma Ruhu da kansa yana yi mana roƙo da nishe-nishen da ba su hurtuwa.
27 t Amma shi mai fayyace zukatanmu ya san abin da Ruhu yake niyya, domin bisa ga nufin Allah ne Ruhu yake yi wa tsarkaka roƙo.Mun Zarce A Ce da Mu Masu Nasara Ne
28 t Mun kuma sani al'amura duka suna aikatawa tare, zuwa alheri ga waɗanda suke ƙaunar Allah, wato, waɗanda suke kirayayyu bisa ga nufinsa. 29 t Waɗanda Allah ya riga ya zaɓa tun tuni, su ne ya ƙaddara su ɗauki kamannin Ɗansa, domin shi Ɗan yă zama na farko a cikin 'yan'uwa masu yawa.
30 t Waɗanda ya ƙaddarar nan kuwa, su ne ya kira. Waɗanda ya kira kuwa, su ne ya kuɓutar. Waɗanda ya kuɓutar ɗin kuwa, su ne ya ɗaukaka.
31 t To, me kuma za mu ce a game da haka? Da yake Allah yana goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu? 32 t Shi da bai hana Ɗansa ba, sai ma ya ba da shi saboda mu duka, ashe, ba zai ba mu kome tare da shi hannu sake ba? 33 t Wa zai ɗora wa zaɓaɓɓun Allah laifi? Allah ne yake kuɓutar da su! 34 t Wa zai hukunta su? Almasihu Yesu wanda ya mutu, ko kuwa a ce wanda ya tashi daga matattu, shi ne wanda yake zaune dama ga Allah, shi ne kuwa wanda yake roƙo saboda mu! 35 t Wa zai iya raba mu da ƙaunar da Almasihu yake yi mana? Ƙunci ne? ko masifa? ko tsanani? ko yunwa? ko huntanci? ko hatsari? ko takobi?
36 t Kamar yadda yake a rubuce cewa,
“Saboda kai ne ake kashe mu yini zubur,
An lasafta mu kamar tumakin yanka.”
37 t Duk da haka kuwa a cikin wannan hali duka, har mun zarce ma a ce mana masu nasara, ta wurin wannan da ya ƙaunace mu. 38 t Domin na tabbata, ko mutuwa ce, ko rai, ko mala'iku, ko manyan mala'iku, ko al'amuran yanzu, ko al'amura masu zuwa, ko masu iko, 39 t ko tsawo, ko zurfi, kai, ko kowace irin halitta ma, ba za su iya raba mu da ƙaunar da Allah yake yi mana ta wurin Almasihu Yesu Ubangijinmu ba.
Romans 8
1 There is therefore now no condemnation to them that are in Christ Jesus.2 For the law of the Spirit of life in Christ Jesus made me free from the law of sin and of death.3 For what the law could not do, in that it was weak through the flesh, God, sending his own Son in the likeness of sinful flesh and for sin, condemned sin in the flesh:4 that the ordinance of the law might be fulfilled in us, who walk not after the flesh, but after the Spirit.5 For they that are after the flesh mind the things of the flesh; but they that are after the Spirit the things of the Spirit.6 For the mind of the flesh is death; but the mind of the Spirit is life and peace:7 because the mind of the flesh is enmity against God; for it is not subject to the law of God, neither indeed can it be:8 and they that are in the flesh cannot please God.9 But ye are not in the flesh but in the Spirit, if so be that the Spirit of God dwelleth in you. But if any man hath not the Spirit of Christ, he is none of his.10 And if Christ is in you, the body is dead because of sin; but the spirit is life because of righteousness.11 But if the Spirit of him that raised up Jesus from the dead dwelleth in you, he that raised up Christ Jesus from the dead shall give life also to your mortal bodies through his Spirit that dwelleth in you.12 So then, brethren, we are debtors, not to the flesh, to live after the flesh:13 for if ye live after the flesh, ye must die; but if by the Spirit ye put to death the deeds of the body, ye shall live.14 For as many as are led by the Spirit of God, these are sons of God.15 For ye received not the spirit of bondage again unto fear; but ye received the spirit of adoption, whereby we cry, Abba, Father.16 The Spirit himself beareth witness with our spirit, that we are children of God:17 and if children, then heirs; heirs of God, and joint-heirs with Christ; if so be that we suffer with him, that we may be also glorified with him.18 For I reckon that the sufferings of this present time are not worthy to be compared with the glory which shall be revealed to us-ward.19 For the earnest expectation of the creation waiteth for the revealing of the sons of God.20 For the creation was subjected to vanity, not of its own will, but by reason of him who subjected it, in hope21 that the creation itself also shall be delivered from the bondage of corruption into the liberty of the glory of the children of God.22 For we know that the whole creation groaneth and travaileth in pain together until now.23 And not only so, but ourselves also, who have the first-fruits of the Spirit, even we ourselves groan within ourselves, waiting for our adoption, to wit, the redemption of our body.24 For in hope were we saved: but hope that is seen is not hope: for who hopeth for that which he seeth?25 But if we hope for that which we see not, then do we with patience wait for it.26 And in like manner the Spirit also helpeth our infirmity: for we know not how to pray as we ought; but the Spirit himself maketh intercession for us with groanings which cannot be uttered;27 and he that searcheth the hearts knoweth what is the mind of the Spirit, because he maketh intercession for the saints according to the will of God.28 And we know that to them that love God all things work together for good, even to them that are called according to his purpose.29 For whom he foreknew, he also foreordained to be conformed to the image of his Son, that he might be the firstborn among many brethren:30 and whom he foreordained, them he also called: and whom he called, them he also justified: and whom he justified, them he also glorified.31 What then shall we say to these things? If God is for us, who is against us?32 He that spared not his own Son, but delivered him up for us all, how shall he not also with him freely give us all things?33 Who shall lay anything to the charge of God’s elect? It is God that justifieth;34 who is he that condemneth? It is Christ Jesus that died, yea rather, that was raised from the dead, who is at the right hand of God, who also maketh intercession for us.35 Who shall separate us from the love of Christ? shall tribulation, or anguish, or persecution, or famine, or nakedness, or peril, or sword?36 Even as it is written, For thy sake we are killed all the day long; We were accounted as sheep for the slaughter.37 Nay, in all these things we are more than conquerors through him that loved us.38 For I am persuaded, that neither death, nor life, nor angels, nor principalities, nor things present, nor things to come, nor powers,39 nor height, nor depth, nor any other creature, shall be able to separate us from the love of God, which is in Christ Jesus our Lord.