TIT 2
Koyar da Kyakkyawar Koyarwa
1 t Amma kai kam, sai ka faɗi abin da ya dace da sahihiyar koyarwa. 2 t Dattawa su kasance masu kamunkai, natsattsu, mahankalta, masu sahihiyar bangaskiya, da ƙauna, da kuma jimiri. 3 t Haka kuma, manyan mata su kasance masu keɓaɓɓen hali, ba masu yanke, ko masu jarabar giya ba, su zamana masu koyar da kyakkyawan abu, 4 ta haka su koya wa mata masu ƙuruciya su so mazansu da 'ya'yansu, 5 t su kuma kasance natsattsu, masu tsarkin rai, masu kula da gida, masu alheri, masu biyayya ga mazansu, don kada a kushe Maganar Allah. 6 t Haka kuma, ka gargaɗi samari su yi kamunkai. 7 t Kai ma sai ka zama gurbi na aiki nagari ta kowace hanya, da koyarwarka kana nuna rashin jirkituwa, da natsuwa, 8 t da kuma sahihiyar maganar da ba za a kushe mata ba, don a kunyata abokan hamayya, su rasa hanyar zarginmu. 9 t Bayi su yi biyayya ga iyayengijinsu, su kuma gamsar da su ta kowane hali. Kada su yi tsayayya,
10 t ko taɓe-taɓe, sai dai su riƙi amana sosai, don su ƙawatar da koyarwar Allah Mai Cetonmu ta kowane hali.
11 t Alherin Allah ya bayyana saboda ceton dukkan mutane, 12 t yana koya mana mu ƙi rashin bin Allah da mugayen sha'awace-sha'awacen duniya, mu kuma yi zamanmu a duniyar nan da natsuwa, da adalci, da kuma bin Allah, 13 t muna sauraron cikar begen nan mai albarka, wato bayyanar ɗaukakar Allahnmu Mai Girma, Mai Cetonmu Yesu Almasihu,
14 t wanda ya ba da kansa dominmu, domin ya fanso mu daga dukan mugun aiki, ya kuma tsarkake jama'a su zama abin mulkinsa, masu himmar yin kyakkyawan aiki.
15 Ka yi ta sanar da waɗannan abubuwa, kana gargaɗar da su, kana tsawatarwa da ƙaƙƙarfan umarni. Kada ka yarda kowa yă raina ka.
Titus 2
1 But speak thou the things which befit the sound doctrine:2 that aged men be temperate, grave, sober-minded, sound in faith, in love, in patience:3 that aged women likewise be reverent in demeanor, not slanderers nor enslaved to much wine, teachers of that which is good;4 that they may train the young women to love their husbands, to love their children,5 to be sober-minded, chaste, workers at home, kind, being in subjection to their own husbands, that the word of God be not blasphemed:6 the younger men likewise exhort to be sober-minded:7 in all things showing thyself an ensample of good works; in thy doctrine showing uncorruptness, gravity,8 sound speech, that cannot be condemned; that he that is of the contrary part may be ashamed, having no evil thing to say of us.9 Exhort servants to be in subjection to their own masters, and to be well-pleasing to them in all things; not gainsaying;10 not purloining, but showing all good fidelity; that they may adorn the doctrine of God our Saviour in all things.11 For the grace of God hath appeared, bringing salvation to all men,12 instructing us, to the intent that, denying ungodliness and worldly lusts, we should live soberly and righteously and godly in this present world;13 looking for the blessed hope and appearing of the glory of the great God and our Saviour Jesus Christ;14 who gave himself for us, that he might redeem us from all iniquity, and purify unto himself a people for his own possession, zealous of good works.15 These things speak and exhort and reprove with all authority. Let no man despise thee.